Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 2:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ni kuwa ina riƙe da finjalin sarki. Wata rana a watan Nisan, a shekara ta ashirin ta sarautar sarki Artashate, sa'ad da na kai masa ruwan inabi, sai na ɗauki ruwan inabin, na ba shi. Ni ban taɓa ɓata fuskata a gabansa a dā ba, sai wannan karo.

2. Sai sarki ya tambaye ni, ya ce, “Me ya sa fuskarka ta ɓaci, ga shi, ba ciwo kake yi ba. Ba abin da ya kawo wannan, sai lalle kana baƙin ciki.”Sai na tsorata ƙwarai,

3. na ce wa sarki, “Ranka ya daɗe, me zai hana fuskata ta ɓaci, da yake birni inda makabartar kakannina take ya zama kango, an kuma ƙone ƙofofinsa da wuta?”

4. Sa'an nan sarki ya ce mini, “To, me kake so?”Sai na yi addu'a ga Allah na Sama,

5. sa'an nan na ce wa sarki, “Idan ka yarda, idan kuma na sami tagomashi a wurinka, ya sarki, ka yardar mini in tafi Yahuza, birnin kakannina, inda makabartarsu take domin in sāke gina shi.”

6. Sarki kuwa, a sa'an nan sarauniya tana zaune kusa da shi, ya ce mini, “Kwana nawa za ka yi, yaushe kuma za ka dawo?” Sai na faɗa masa, ya kuwa yardar mini in tafi, ni kuwa na yanka masa kwanakin da zan yi.

7. Sa'an nan na ce wa sarki, “Idan sarki ya yarda, sai a ba ni takarda zuwa ga masu mulki da suke a lardin Yammacin Kogin Yufiretis domin su yardar mini in wuce zuwa Yahuza.

8. A kuma ba ni takarda zuwa ga Asaf, sarkin daji, domin ya ba ni katakan da zan yi jigajigan ƙofofin kagarar Haikali, da na garun birnin, da na gidan da zan zauna.” Sarki kuwa ya ba ni abin da na roƙa, gama Allah yana tare da ni.

9. Da na zo wurin masu mulkin Yammacin Kogin Yufiretis, sai na miƙa musu takardar sarki. Sarki ya haɗa ni da sarkin yaƙi da mahayan dawakai.

Karanta cikakken babi Neh 2