Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 31:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Musa ya ci gaba da yi wa dukan Isra'ilawa magana.

2. Ya ce, “Yau shekarata ɗari da ashirin ne, ba na iya kaiwa da komowa. Ubangiji kuwa ya ce mini, ‘Ba za ka haye wannan Urdun ba.’

3. Ubangiji Allahnku shi ne zai yi gaba ya haye, ya hallaka al'umman da take gabanku don ku ci su. Joshuwa ne zai shugabance ku, ya haye kamar yadda Ubangiji ya faɗa.

4. Ubangiji zai yi musu kamar yadda ya yi wa Sihon da Og, sarakunan Amoriyawa, da ƙasarsu, sa'ad da ya hallaka su.

5. Ubangiji zai bashe su a gare ku. Za ku yi musu kamar yadda dā na umarce ku.

6. Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.”

7. Sai Musa ya kira Joshuwa, ya yi masa magana a gaban dukan jama'ar Isra'ila, ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai wannan jama'a cikin ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninsu. Kai ne za ka ba su ita gādo.

8. Ubangiji kansa zai bi da kai, ba zai kunyatar da kai ba, ba kuwa zai yashe ka ba. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karai.”

9. Sai Musa ya rubuta waɗannan dokoki, ya ba firistoci, 'ya'yan Lawiyawa, waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawari na Ubangiji, da dukan dattawan Isra'ila.

10. Sai Musa ya umarce su, ya ce, “A ƙarshen kowace shekara bakwai, a lokacin da aka ƙayyade na shekarar yafewa, a lokacin Idin Bukkoki,

11. sa'ad da dukan Isra'ilawa za su hallara a gaban Ubangiji Allahnku a inda zai zaɓa, to, sai ku karanta musu waɗannan dokoki su ji da kunnuwansu.

12. Ku tara dukan jama'a wuri ɗaya, mata da maza, da yara, da baƙin da suke zaune tare da ku a garuruwanku domin su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su kuma lura su aikata dukan dokokin nan,

13. domin 'ya'yansu, waɗanda ba su sani ba, su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku dukan kwanakinku cikin ƙasar da za ku haye Urdun, ku mallaka.”

14. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Lokacin rasuwarka ya yi, sai ka kira Joshuwa, ku shigo alfarwa ta sujada, don in ba shi ragamar mulki.” Sai Musa da Joshuwa suka tafi, suka shiga alfarwa ta sujada.

15. Ubangiji kuwa ya bayyana a cikin alfarwar a al'amudin girgije. Al'amudin girgijen kuwa ya tsaya a ƙofar alfarwar.

Karanta cikakken babi M. Sh 31