Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Joshuwa zai Gāji Musa

1. Sai Musa ya ci gaba da yi wa dukan Isra'ilawa magana.

2. Ya ce, “Yau shekarata ɗari da ashirin ne, ba na iya kaiwa da komowa. Ubangiji kuwa ya ce mini, ‘Ba za ka haye wannan Urdun ba.’

3. Ubangiji Allahnku shi ne zai yi gaba ya haye, ya hallaka al'umman da take gabanku don ku ci su. Joshuwa ne zai shugabance ku, ya haye kamar yadda Ubangiji ya faɗa.

4. Ubangiji zai yi musu kamar yadda ya yi wa Sihon da Og, sarakunan Amoriyawa, da ƙasarsu, sa'ad da ya hallaka su.

5. Ubangiji zai bashe su a gare ku. Za ku yi musu kamar yadda dā na umarce ku.

6. Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.”

7. Sai Musa ya kira Joshuwa, ya yi masa magana a gaban dukan jama'ar Isra'ila, ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai wannan jama'a cikin ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninsu. Kai ne za ka ba su ita gādo.

8. Ubangiji kansa zai bi da kai, ba zai kunyatar da kai ba, ba kuwa zai yashe ka ba. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karai.”

A Karanta Dokokin Kowace Shekara ta Bakwai

9. Sai Musa ya rubuta waɗannan dokoki, ya ba firistoci, 'ya'yan Lawiyawa, waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawari na Ubangiji, da dukan dattawan Isra'ila.

10. Sai Musa ya umarce su, ya ce, “A ƙarshen kowace shekara bakwai, a lokacin da aka ƙayyade na shekarar yafewa, a lokacin Idin Bukkoki,

11. sa'ad da dukan Isra'ilawa za su hallara a gaban Ubangiji Allahnku a inda zai zaɓa, to, sai ku karanta musu waɗannan dokoki su ji da kunnuwansu.

12. Ku tara dukan jama'a wuri ɗaya, mata da maza, da yara, da baƙin da suke zaune tare da ku a garuruwanku domin su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su kuma lura su aikata dukan dokokin nan,

13. domin 'ya'yansu, waɗanda ba su sani ba, su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku dukan kwanakinku cikin ƙasar da za ku haye Urdun, ku mallaka.”

Umarnin Ƙarshe da Ubangiji Ya Yi wa Musa

14. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Lokacin rasuwarka ya yi, sai ka kira Joshuwa, ku shigo alfarwa ta sujada, don in ba shi ragamar mulki.” Sai Musa da Joshuwa suka tafi, suka shiga alfarwa ta sujada.

15. Ubangiji kuwa ya bayyana a cikin alfarwar a al'amudin girgije. Al'amudin girgijen kuwa ya tsaya a ƙofar alfarwar.

16. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ga shi, za ka rasu ka tarar da kakanninka. Wannan jama'a kuwa za ta fara kaucewa daga hanya, su bi gumakan ƙasar da za su shiga, su zauna. Za su rabu da ni, su ta da alkawarina wanda na yi da su.

17. A wannan rana zan husata da su ƙwarai, in rabu da su, in ɓoye musu fuskata, za a cinye su. Masifu da wahalai za su same su. Za su kuwa ce a ranar, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu.’

18. Hakika kuwa, zan ɓoye musu fuskata sabili da muguntar da suka aikata, suka kuma bi gumaka.

19. “Don haka, sai ka rubuta wannan waƙa, ka koya wa Isra'ilawa. Ka sa ta a bakinsu don waƙan nan ta zama shaida a gare ni game da Isra'ilawa.

20. Sa'ad da na kawo su a ƙasar da take da yalwar abinci, wadda na rantse zan ba kakanninsu, har suka ci, suka ƙoshi, suka yi ƙiba, za su juya, su bi gumaka, su bauta musu. Za su raina ni, su tā da alkawarina.

21. Sa'ad da yawan masifun nan da wahalan nan suka same su, to, waƙar nan za ta ba da shaida a kansu, gama zuriyarsu ba za ta manta da wannan waƙa ba, gama na san ƙudurin da suke yi kafin in kawo su ƙasar da na rantse zan bayar.”

22. Saboda wannan sai Musa ya rubuta wannan waƙa a ranar, ya koya wa jama'ar Isra'ila.

23. Sai Ubangiji ya umarci Joshuwa ɗan Nun ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai jama'ar Isra'ila a ƙasar da na rantse zan ba su, ni kuma da kaina zan tafi tare da kai.”

24. Sa'ad da Musa ya gama rubuta maganar dokokin nan sarai a littafin,

25. sai ya umarci Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, ya ce,

26. “Ku ɗauki littafin dokokin nan, ku ajiye shi tare da akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku domin ya zama shaida a kanku,

27. gama na san tayarwarku da taurinkanku. Tun ma ina da rai ke nan tare da ku kuka tayar wa Ubangiji, balle bayan rasuwata.

28. Ku tattaro mini dattawan kabilanku da manyanku don in faɗa musu wannan magana a kunnensu, in kuma kira sama da duniya su zama shaida a kansu.

29. Gama na sani bayan rasuwata za ku aikata mugunta, ku kauce daga hanyar da na umarce ku. Masifa za ta auko muku a kwanaki masu zuwa saboda za ku aikata mugunta a gaban Ubangiji, za ku tsokani fushinsa da aikin hannuwanku.”

Waƙar Musa

30. Sa'an nan Musa ya hurta kalmomin wannan waƙa a kunnen dukan taron jama'ar Isra'ila har ƙarshensu.