Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 7:12-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Saboda haka Isra'ilawa ba su iya tsayawa a gaban abokan gābansu ba, sun ba da baya ga abokan gābansu, gama sun zama haramtattu don hallakarwa. Daɗai, ba zan kasance tare da ku ba, sai dai kun kawar da haramtattun abubuwa da suke cikinku.

13. Tashi, ka tsarkake jama'a, ka ce, ‘Ku tsarkake kanku domin gobe, gama Ubangiji, Allah na Isra'ila ya ce akwai haramtattun abubuwa a tsakiyarku. Ya Isra'ila, ba ku iya tsayawa a gaban abokan gābanku ba, sai kun kawar da haramtattun abubuwa daga tsakiyarku.

14. Da safe kuwa za a gabatar da ku kabila kabila, zai zama kuwa kabilar da Ubangiji ya ware, za a gabatar da ita iyali iyali, iyalin da Ubangiji ya ware kuma, za a gabatar da su gida gida, gidan kuma da Ubangiji ya ware, za a gabatar da su mutum mutum.

15. Zai zama kuwa wanda aka same shi da haramtattun abubuwa, za a ƙone shi da wuta, shi da dukan abin da yake da shi, domin ya tā da alkawarin Ubangiji, ya kuma yi abin kunya cikin Isra'ila.’ ”

16. Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, ya gabatar da Isra'ilawa kabila kabila, aka ware kabilar Yahuza.

17. Ya gabatar da iyalan Yahuza, aka ware iyalin Zera. Ya gabatar da iyalin Zera gida gida, aka ware gidan Zebdi.

18. Ya gabatar da iyalin gidansa mutum mutum, aka ware Akan, ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera na kabilar Yahuza.

19. Sai ya ce wa Akan, “Ɗana, ka ba da girma ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka yabe shi ka gaya mini abin da ka yi, kada ka ɓoye mini.”

20. Akan kuwa ya amsa wa Joshuwa, ya ce, “A gaskiya kam, na yi wa Ubangiji, Allah na Isra'ila zunubi. Ga abin da na yi.

21. A cikin kayan ganimar na ga wata kyakkyawar alkyabba irin ta Shinar, da shekel dari biyu na azurfa, da sandan zinariya mai nauyin shekel hamsin, sai na yi ƙyashi, na kwashe su, ga su a binne a ƙasa a alfarwata da azurfa a ƙarƙashi.”

22. Joshuwa ya aika da manzanni, suka sheƙa a guje zuwa alfarwar, suka tarar da abubuwan a binne cikin alfarwarsa da azurfa a ƙarƙashi.

23. Sai suka kwaso suka kawo wa Joshuwa da dukan Isra'ilawa, suka ajiye su a gaban Ubangiji.

24. Joshuwa kuwa tare da dukan Isra'ilawa suka ɗauki Akan, ɗan Zera, da azurfar, da alkyabbar, da sandan zinariya, da 'ya'yansa mata da maza, da shanunsa, da jakunansa, da tumakinsa, da alfarwarsa, da dukan abin da yake da shi, suka kawo su a Kwarin Akor.

25. Sai Joshuwa ya ce, “Don me ka wahalshe mu? Kai ma, Ubangiji zai wahalshe ka yau!” Dukan Isra'ilawa suka jajjefe su da duwatsu, suka ƙone su da wuta.

26. Suka tara tsibin duwatsu a kansu. Tsibin duwatsun kuwa yana nan har wa yau. Sa'an nan Ubangiji ya huce daga zafin fushinsa. Domin haka ana kiran wurin Kwarin Akor, wato azaba, har wa yau.

Karanta cikakken babi Josh 7