Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 60:14-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. 'Ya'ya maza na waɗanda suka zalunce ki za su zo,Su rusuna, su nuna bangirma.Dukan waɗanda suka raina ki za su yi sujada a ƙafafunki.Za su ce da ke, ‘Birnin Ubangiji,’‘Sihiyona, Birni na Allah Mai Tsarki na Isra'ila.’

15. “Ba za a ƙara ƙinki, a yashe ki ba,Ki zama birnin da aka fita aka bari ba kowa ciki.Zan sa ki zama babba, mai ƙayatarwa kuma,Wurin yin farin ciki har abada abadin.

16. Al'ummai da sarakuna za su lura da keKamar yadda uwa take lura da ɗanta.Za ki sani, ni Ubangiji, na cece ki,Allah Mai Iko Dukka na Isra'ila ya fanshe ki.

17. “Zan kawo miki zinariya maimakon tagulla,Azurfa maimakon baƙin ƙarfe,Tagulla kuma maimakon itace.Za ki sami baƙin ƙarfe maimakon dutse.Masu mulkinki ba za ƙara zaluntarki ba,Zan sa su yi mulki da gaskiya da salama.

18. Ba za a ƙara jin hayaniyar tashin hankali ba,Ba za a ƙara aukar wa ƙasar da ɓarna ba.Zan kiyaye ki, in kāre ki kamar garu,Za ki yi yabona domin na cece ki.

19. “Rana ba za ta ƙara zama haskenki da rana ba,Ko wata ya zama haskenki da dare.Ni, Ubangiji, zan zama madawwamin haskenki,Hasken ɗaukakata zai haskaka a kanki.

20. Kwanakin baƙin cikinki za su ƙare.Ni, Ubangiji, zan zama madawwamin haskenki,Mai daɗewa fiye da na rana da na wata.

21. Dukan mutanenki za su yi abin da yake daidai,Za su kuwa mallaki ƙasar har abada.Ni na dasa su, ni na yi suDomin su bayyana girmana ga duka.

22. Har ma da iyalin da suka fi ƙanƙanta da ƙasƙanci,Za su zama babbar al'umma,Kamar al'umma mai iko.Zan sa wannan ya faru nan da nanSa'ad da lokacin da ya dace ya yi.Ni ne Ubangiji!”

Karanta cikakken babi Ish 60