Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 44:9-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Dukan waɗanda suke ƙera gumaka mutanen banza ne, gumakan da suke sa wa kuɗi da tsada kuma aikin banza ne. Waɗanda suke yi wa gumaka sujada kuwa makafi ne su, jahilai, za su sha kunya.

10. Wannan aikin banza ne, mutum ya yi siffa da ƙarfe don ya yi mata sujada!

11. Dukan wanda ya yi mata sujada za a ƙasƙantar da shi. Mutanen da suka ƙera gumakan, 'yan adam ne, ba wani abu ba. Bari su zo su tsaya gaban shari'a, za su razana, su kuma sha kunya.

12. Maƙeri yakan ɗauki guntun ƙarfe ya sa shi a wuta ya yi aiki. Da hannunsa mai ƙarfi yana ɗaukar guduma yana bugun ƙarfen, yana mai da shi siffa. Yakan ji yunwa, da ƙishi, yakan kuma ji gajiya.

13. Masassaƙi yakan auna itace. Ya zana siffa da alli, sa'an nan ya sassaƙe shi da kayan aikinsa. Ya yi shi da siffar mutum kyakkyawa, domin a ajiye shi a masujadarsu.

14. Zai yiwu ya sare itacen al'ul ya yi da shi, ko kuwa ya zaɓi itacen oak, ko na kasharina daga jeji. Ko kuwa ya dasa wani itace, ya jira ruwan sama don ya sa itacen ya yi girma.

15. Mutum yakan yi abin wuta da wani sashi na itacen, wani sashi kuma ya yi gunki da shi. Yakan hura wuta da wani sashi don ya ji ɗumi, yakan kuma toya gurasa. Yakan yi gunki da wani sashi, ya riƙa yi masa sujada!

16. Yakan hura wuta da wani sashi domin ya gasa nama, ya ci, ya ƙoshi. Ya ji ɗumi ya ce, “Kai, ɗumi da daɗi, wutar tana da kyau!”

17. Sauran itacen ya mai da shi gunki. Yana rusunawa ya yi masa sujada. Yana addu'a gare shi yana cewa, “Kai ne Allahna, ka cece ni!”

18. Irin waɗannan mutane dakikai ne, har ba su san abin da suke yi ba. Sun rufe idanunsu da tunaninsu ga gaskiya.

19. Masu ƙera gumaka ba su da ko tunanin da za su ce, “Na ƙone wani sashi na itacen nan. Na toya gurasa a garwashin, na kuma gasa nama, na ci shi, na kuwa ce sauran itacen zan sassaƙa gunki da shi. Ga ni yanzu, ina ta rusunawa gaban guntun itace!”

20. Ya zama daidai kamar mutum ya ci toka. Manufarsa ta wauta ta ɓatar da shi, har ba yadda za a iya taimakonsa. Ba zai iya ganewa ba, gunkin da ya riƙe a hannunsa ba allah ba ne ko kaɗan.

21. Ubangiji ya ce,“Ka tuna da waɗannan abu, ya Isra'ila,Ka tuna kai bawana ne.Na halicce ka domin ka zama bawana,Ba zan taɓa mantawa da kai ba.

22. Na shafe zunubanka kamar baƙin girgije,Da girgije kuma zan rufe laifofinkaKa komo wurina, ni ne na fanshe ka.”

Karanta cikakken babi Ish 44