Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 4:25-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Za a kore ka daga cikin mutane zuwa jeji ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka sani Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.

26. Kamar yadda aka umarta a bar kututturen itacen da saiwoyinsa, haka nan za a tabbatar maka da sarautarka sa'ad da ka gane Mai Sama ne yake mulki.

27. Saboda haka, ya sarki, sai ka karɓi shawarata, ka daina zunubanka, ka yi adalci. Ka bar muguntarka, ka aikata alheri ga waɗanda ake wulakantawa, watakila za a ƙara tsawon kwanakinka da salama.”

28. Wannan duka kuwa ya sami sarki Nebukadnezzar.

29. Bayan wata goma sha biyu, sa'ad da yake yawatawa a kan benen fādar Babila,

30. sai ya ce, “Ashe, wannan ba ita ce Babila babba wadda ni da kaina na gina, da ƙarfin ikona don ta zama fādar sarauta, don darajar ɗaukakata?”

31. Kafin sarki ya rufe baki sai ga murya daga sama, tana cewa, “Ya sarki Nebukadnezzar, da kai ake magana, yanzu an tuɓe ka daga sarauta.

32. Za a kuma kore ka daga cikin mutane zuwa jeji, ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka gane Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.”

33. Nan take sai abin da aka faɗa a kan Nebukadnezzar ya tabbata. Aka kore shi daga cikin mutane. Ya shiga cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har gashinsa ya yi tsawo kamar gashin gaggafa, akaifunsa kuma suka yi tsawo kamar na tsuntsu.

34. “A ƙarshen kwanakin, sai ni Nebukadnezzar, na ɗaga ido sama, sai hankalina ya komo mini, na ɗaukaka Maɗaukaki, na yabe shi, na girmama shi wanda yake rayayye har abada.“Gama mulkinsa madawwamin mulki ne,Sarautarsa kuwa daga zamani zuwa zamani.

35. Dukan mazaunan duniya ba a bakin kome suke a gare shi ba.Yakan yi yadda ya nufa da rundunar sama da mazaunan duniya,Ba mai hana shi, ba kuma mai ce masa, ‘Me kake yi?’

36. “A lokacin nan hankalina ya komo mini, sai aka mayar mini da masarautata mai daraja, da martabata, da girmana. 'Yan majalisata da fādawana suka nemo ni. Aka maido ni kan gadon sarautata da daraja fiye da ta dā.

37. Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin Samaniya, ina ɗaukaka shi, ina kuma girmama shi saboda dukan ayyukansa daidai ne, al'amuransa kuma gaskiya ne. Yakan ƙasƙantar da masu girmankai.”

Karanta cikakken babi Dan 4