Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Haukar Nebukadnezzar

1. “Daga sarki Nebukadnezzar zuwa ga dukan mutane, da al'ummai, da harsuna mabambanta waɗanda suke zaune a duniya duka. Salama mai yawa ta tabbata a gare ku!

2. Na ga ya yi kyau in sanar muku da alamu da abubuwan al'ajabi waɗanda Allah Maɗaukaki ya nuna mini.

3. “Alamunsa da girma suke!Al'ajabansa da bantsoro suke!Sarautarsa ta har abada ce,Mulkinsa kuma daga zamani zuwa zamani ne.

4. “Ni, Nebukadnezzar ina cikin gidana, ina nishaɗi a fādata.

5. Sa'ad da nake kwance a gādona, sai na yi mafarki wanda ya tsorata ni. Tunanina da wahayi suka firgitar da ni.

6. Don haka na umarta a kirawo mini dukan masu hikima na Babila don su yi mini fassarar mafarkin.

7. Sai masu sihiri, da masu dabo, da Kaldiyawa, da masu duba suka zo, na faɗa musu mafarkin, amma ba su iya yi mini fassararsa ba.

8. Daga baya sai Daniyel wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, wato irin sunan allahna, yana kuwa da ruhun alloli tsarkaka, ya shigo wurina. Na kuwa faɗa masa mafarkin, na ce,

9. ‘Ya Belteshazzar shugaban masu sihiri, tun da yake na san ruhun alloli tsarkaka yana a cikinka, ba wani asirin da zai fi ƙarfin ganewarka. Ga mafarkin da na yi, sai ka faɗa mini fassararsa.

10. “ ‘Wahayin da na gani ke nan sa'ad da nake kwance a gadona. Na ga wani itace mai tsayi ƙwarai a tsakiyar duniya.

11. Itacen ya yi girma, ya ƙasaita,Ƙwanƙolinsa ya kai har sama,Ana iya ganinsa ko'ina a duniya.

12. Yana da ganyaye masu kyauDa 'ya'ya jingim don kowa da kowa ya ci.Namomin jeji suka sami inuwa a ƙarƙashinsa,Tsuntsayen sama kuma suka zauna a rassansa.Dukan masu rai a gare shi suka sami abinci.

13. “ ‘A cikin wahayin da na gani sa'ad da nake kwance a gado, sai ga wani mai tsaro, tsattsarka, ya sauko daga sama.

14. Sai ya yi magana da ƙarfi, ya ce,“A sare itacen, a daddatse rassansa,A zage ganyayensa ƙaƙaf, a warwatsar da 'ya'yansa.A sa namomin jeji su gudu daga ƙarƙashinsa,Tsuntsaye kuma su tashi daga rassansa.

15. Amma a bar kututturen da saiwoyinsa a ƙasaƊaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla.A bar shi can cikin ɗanyar ciyawar saura,Ya jiƙe da raɓa,Ya yi ta cin ciyawa tare da namomin jeji.

16. A raba shi da hankali irin na mutane,A ba shi irin na dabba.Zai zauna a wannan hali har shekara bakwai.

17. Wannan shi ne hukuncin da tsarkaka,Masu tsaro suka shawarta,Suka yanke domin masu rai su saniMaɗaukaki yake sarautar 'yan adam,Yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama,Yakan sa talaka ya zama sarki.”

18. “ ‘Mafarkin da ni sarki Nebukadnezzar na yi ke nan. Kai Belteshazzar kuma, sai ka faɗa mini ma'anarsa, domin dukan masu hikima na cikin mulkina ba su iya faɗar mini ma'anar, amma kai ka iya, gama ruhun alloli tsarkaka yana cikinka.’ ”

Daniyel Ya Faɗi Ma'anar Mafarkin

19. Daniyel kuwa wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, ya tsaya zugum da ɗan daɗewa, tunaninsa ya ba shi tsoro. Sarki ya ce, “Belteshazzar, kada ka bar mafarkin ko ma'anarsa ya ba ka tsoro.”Sai Belteshazzar ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, Allah ya sa mafarkin nan, da ma'anarsa, su zama a kan maƙiyanka.

20. Itacen nan da ka gani wanda ya yi girma, ya ƙasaita, ƙwanƙolinsa ya kai sama, har ana iya ganinsa daga ko'ina a duniya,

21. yana da ganyaye masu kyau da 'ya'ya jingim don kowa da kowa ya ci, namomin jeji suka sami inuwa a ƙarƙashinsa, tsuntsaye kuma suka zauna a rassansa,

22. kai ne wannan itace, ya sarki. Ka yi girma, ka ƙasaita. Girmanka ya kai har sama, mulkinka kuma ya kai ko'ina a duniya.

23. Ka kuma ga mai tsaro tsattsarka yana saukowa daga sama, yana cewa a sare itacen nan, a ragargaje shi, amma a bar kututturen da saiwoyinsa cikin ƙasa ɗaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla. An ce a bar shi can a ɗanyar ciyawar saura, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namomin jeji har shekara bakwai.

24. “Ga ma'anarsa, ya sarki, wannan ƙaddara ce wadda Maɗaukaki zai aukar wa shugabana sarki da ita.

25. Za a kore ka daga cikin mutane zuwa jeji ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka sani Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.

26. Kamar yadda aka umarta a bar kututturen itacen da saiwoyinsa, haka nan za a tabbatar maka da sarautarka sa'ad da ka gane Mai Sama ne yake mulki.

27. Saboda haka, ya sarki, sai ka karɓi shawarata, ka daina zunubanka, ka yi adalci. Ka bar muguntarka, ka aikata alheri ga waɗanda ake wulakantawa, watakila za a ƙara tsawon kwanakinka da salama.”

28. Wannan duka kuwa ya sami sarki Nebukadnezzar.

29. Bayan wata goma sha biyu, sa'ad da yake yawatawa a kan benen fādar Babila,

30. sai ya ce, “Ashe, wannan ba ita ce Babila babba wadda ni da kaina na gina, da ƙarfin ikona don ta zama fādar sarauta, don darajar ɗaukakata?”

31. Kafin sarki ya rufe baki sai ga murya daga sama, tana cewa, “Ya sarki Nebukadnezzar, da kai ake magana, yanzu an tuɓe ka daga sarauta.

32. Za a kuma kore ka daga cikin mutane zuwa jeji, ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka gane Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.”

33. Nan take sai abin da aka faɗa a kan Nebukadnezzar ya tabbata. Aka kore shi daga cikin mutane. Ya shiga cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har gashinsa ya yi tsawo kamar gashin gaggafa, akaifunsa kuma suka yi tsawo kamar na tsuntsu.

Nebukadnezzar Ya Yabi Allah

34. “A ƙarshen kwanakin, sai ni Nebukadnezzar, na ɗaga ido sama, sai hankalina ya komo mini, na ɗaukaka Maɗaukaki, na yabe shi, na girmama shi wanda yake rayayye har abada.“Gama mulkinsa madawwamin mulki ne,Sarautarsa kuwa daga zamani zuwa zamani.

35. Dukan mazaunan duniya ba a bakin kome suke a gare shi ba.Yakan yi yadda ya nufa da rundunar sama da mazaunan duniya,Ba mai hana shi, ba kuma mai ce masa, ‘Me kake yi?’

36. “A lokacin nan hankalina ya komo mini, sai aka mayar mini da masarautata mai daraja, da martabata, da girmana. 'Yan majalisata da fādawana suka nemo ni. Aka maido ni kan gadon sarautata da daraja fiye da ta dā.

37. Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin Samaniya, ina ɗaukaka shi, ina kuma girmama shi saboda dukan ayyukansa daidai ne, al'amuransa kuma gaskiya ne. Yakan ƙasƙantar da masu girmankai.”