Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 3:16-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Shadrak, da Meshak, da Abed-nego kuwa suka amsa wa sarki suka ce, “Ya maigirma Nebukadnezzar, ba mu bukatar mu amsa maka da kome a kan wannan al'amari.

17. Idan haka ne, Allahnmu wanda muke bauta wa, yana da iko ya cece mu daga tanderun gagarumar wuta, zai kuwa kuɓutar da mu daga hannunka, ya sarki.

18. Ko ma bai cece mu ba, ka sani fa ya sarki, ba za mu bauta wa allolinka, ko kuma mu yi wa gunkin zinariya da ka kafa sujada ba.”

19. Sai Nebukadnezzar ya husata ƙwarai da Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, har fuskarsa ta sāke. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar, har sau bakwai fiye da yadda take a dā.

20. Sa'an nan ya umarci waɗansu ƙarfafan mutane daga cikin sojojinsa su ɗaure Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, su jefa su a tanderun gagarumar wuta.

21. Sai aka ɗaure su suna saye da rigunansu da wandunansu, da hulunansu, da sauran tufafinsu, aka jefa su a tanderun gagarumar wuta.

22. Tsananin umarnin sarki ya sa aka haɓaka wutar, sai harshen wutar ya kashe waɗanda suka jefa su Shadrak, da Meshak, da Abed-nego cikin wutar.

23. Sa'an nan mutanen nan uku, wato Shadrak, da Meshak, da Abed-nego suka faɗi a tanderun gagarumar wuta a ɗaure.

24. Sarki Nebukadnezzar kuwa ya zabura ya miƙe tsaye, cike da mamaki. Ya ce wa manyan fādawansa, “Ashe, ba mutum uku ne muka jefa a wuta ba?”Su kuwa suka amsa wa sarki suka ce, “Ba shakka, haka yake, ranka ya daɗe.”

25. Sarki ya ce, “Amma ina ganin mutum huɗu a sake, suna tafiya a tsakiyar wuta, ba kuma abin da ya same su, kamannin na huɗun kuwa kamar na ɗan alloli.”

26. Nebukadnezzar fa ya matso kusa da ƙofar tanderun gagarumar wuta, ya ce, “Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, bayin Allah Maɗaukaki, ku fito, ku zo nan!” Sai Shadrak, da Meshak, da Abed-nego suka fita daga cikin wutar.

27. Sa'an nan su hakimai, da wakilai, da muƙaddasai, da manyan 'yan majalisa suka taru, suka ga lalle wutar ba ta yi wa jikunan mutanen nan lahani ba, gashin kawunansu bai ƙuna ba, tufafinsu ba su ci wuta ba, ko warin wuta babu a jikinsu.

28. Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, wanda ya aiko da mala'ikansa, ya ceci bayinsa masu dogara gare shi, waɗanda kuma ba su yarda su bi umarnin sarki ba, amma suka gwammace a ƙone su maimakon su bauta wa gunki, ko su yi masa sujada, sai dai ga Allahnsu kaɗai.

29. Domin haka ina ba da wannan umarni cewa, ‘Dukan jama'a, ko al'umma, ko harshe wanda zai yi saɓon Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, za a yanyanka su gunduwa gunduwa, a ragargaje gidajensu, gama ba wani allah wanda zai yi wannan irin ceto.’ ”

30. Sa'an nan sarki ya ƙara wa Shadrak, da Meshak, da Abed-nego girma a lardin Babila.

Karanta cikakken babi Dan 3