Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 7:9-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. A rana ta takwas kuwa suka yi wani muhimmin taro, domin su keɓe bagaden. Sun yi kwana bakwai suna yin bikin.

10. A ran ashirin da uku ga watan bakwai, sai sarki ya sallami jama'a su koma gidajensu, suna ta murna da farin ciki a zuciyarsu saboda alherin da Ubangiji ya nuna wa Dawuda, da Sulemanu, da kuma jama'arsa Isra'ila.

11. Haka kuwa Sulemanu ya gama Haikalin Ubangiji da fādar sarki. Ya fa yi nasara cikin dukan irin abin da ya yi niyya game da Haikalin Ubangiji da fādarsa.

12. Sa'an nan Ubangiji ya bayyana ga Sulemanu da dare, ya ce masa, “Na ji addu'arka, na kuwa zaɓi wannan wuri domin kaina, domin ya zama Haikalin miƙa hadaya.

13. Har idan na kulle sammai yadda ba za a yi ruwan sama ba, ko kuma in umarci fara su cinye ƙasar, ko kuwa in aiko da annoba cikin jama'ata,

14. in jama'ata waɗanda ake kiransu da sunana za su yi tawali'u, su yi addu'a, su nemi fuskata, su juyo su bar mugayen ayyukansu, sa'an nan sai in ji su daga Sama, in gafarta zunubansu, in kuma warkar da ƙasarsu.

15. Yanzu idanuna za su kasance a buɗe, kunnuwana kuma za su saurari addu'ar da za a yi a wannan wuri.

16. Yanzu fa na riga na zaɓi wannan Haikali, na kuwa keɓe shi domin sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata kuma za su kasance a wurin kullayaumin.

17. Amma kai, idan za ka yi zamanka a gabana kamar yadda tsohonka Dawuda ya yi, ka kuma aikata bisa ga dukan abin da na umarce ka, ka kiyaye dokokina da farillaina,

18. to, zan kafa gadon sarautarka, yadda na alkawarta wa tsohonka Dawuda, cewa ba za a rasa mutumin da zai yi mulkin Isra'ila ba.

19. Amma idan ka juya, ka bar dokokina da umarnaina waɗanda na sa a gabanka, har ka shiga bautar gumaka kana musu sujada,

20. to, sai in tumɓuke ka daga ƙasata wadda na ba ka, wannan Haikali kuma wanda na riga na keɓe domin sunana, zan kawar da shi daga fuskata, zan kuwa maishe shi abin karin magana, abin raini ga dukan sauran al'umma.

Karanta cikakken babi 2 Tar 7