Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 32:21-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Ubangiji kuwa ya aiki mala'ika wanda ya karkashe manyan jarumawa, da sarakunan yaƙi, da shugabanni, da kowane riƙaƙƙen soja, da sarkin yaƙi da yake a sansanin Sarkin Assuriya. Sai ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa'ad da ya shiga gidan gunkinsa, sai waɗansu daga cikin 'ya'yan cikinsa suka kashe shi da takobi.

22. Ta haka Ubangiji ya ceci Hezekiya da mazaunan Urushalima daga hannun Sennakerib Sarkin Assuriya, daga kuma hannun dukan maƙiyansa, ya hutar da su ta kowace fuska.

23. Mutane da yawa suka kawo wa Ubangiji sadakoki a Urushalima, suna kuma kawo wa Hezekiya Sarkin Yahuza abubuwa masu daraja. Saboda haka ya sami ɗaukaka a idon dukan sauran al'ummai, tun daga wannan lokaci har zuwa gaba.

24. A kwanakin nan kuwa Hezekiya ya yi ciwo gab da mutuwa, sai ya yi addu'a ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya amsa masa ya ba shi alama.

25. Amma Hezekiya bai nuna godiya a kan amfanin da ya samu ba, saboda girmankai. Saboda haka hasala ta auka kansa, da kan Yahuza da Urushalima.

26. Amma Hezekiya ya ƙasƙantar da kansa saboda girmankan da ya yi, shi da mazaunan Urushalima, saboda haka hasalar Ubangiji ba ta faɗa musu a kwanakin Hezekiya ba.

27. Hezekiya yana da dukiya ƙwarai, yana kuma da girma. Sai ya gina wa kansa taskoki inda zai ajiya azurfa, da zinariya, da duwatsu masu daraja, da kayan yaji, da garkuwoyi, da dukan tasoshi, da kwanoni masu daraja.

28. Yana kuma da ɗakunan ajiya na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai. Yana da wuraren turke shanu na kowane iri, yana kuma da garkunan tumaki.

29. Ya kuma giggina wa kansa birane, yana da garkunan tumaki da na awaki, da na shanu a yalwace. Gama Allah ya mallakar masa da abubuwa masu yawa.

30. Hezekiyan nan kuwa ya datse ruwan da yake gangarawa daga kogin Gihon, ya karkatar da su su gangara zuwa wajen yammacin birnin Dawuda. Hezekiya ya arzuta da dukan ayyukan da ya yi.

31. A kan 'yan saƙon sarakunan Babila kuwa, waɗanda aka aiko su don su bincika irin abin al'ajabi da ya faru a ƙasar, sai Allah ya ƙyale shi kurum don ya jarraba shi, ya san dukan abin da suke a zuciyarsa.

32. Sauran ayyukan Hezekiya da kyawawan ayyukansa, ga shi, an rubuta su a wahayin annabi Ishaya ɗan Amoz, a littafin sarakunan Yahuza da na Isra'ila.

Karanta cikakken babi 2 Tar 32