Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 20:21-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Sa'ad da ya yi shawara da jama'a, sai ya zaɓi waɗanda za su raira waƙa ga Ubangiji, su yabe shi a natse sa'ad da suke tafe a gaban runduna, su ce,“Ku yi godiya ga Ubangiji,Saboda madawwamiyar ƙaunarsaTabbatacciya ce har abada.”

22. Sa'ad da suka fara raira waƙa, suna yabo, sai Ubangiji ya sa wa mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, 'yan kwanto, 'yan kwanton kuwa suka fatattake su.

23. Gama mutanen Ammon da na Mowab suka tasar wa mazaunan Dutsen Seyir, suka hallaka su ƙaƙaf. Sa'ad da suka karkashe mazaunan Seyir sai suka fāɗa wa juna, suka yi ta hallaka kansu da kansu.

24. Da mutanen Yahuza suka zo hasumiyar tsaro ta jeji, suka duba sai suka ga gawawwaki kawai a kwance, ba wanda ya tsira.

25. Sa'ad da Yehoshafat da jama'arsa suka je kwasar ganima, sai suka sami shanu masu yawan gaske, da kayayyaki, da tufafi, da abubuwa masu daraja, waɗanda suka yi ta kwasa har suka gaji. Kwana uku suka yi suna ta kwasar ganimar saboda yawanta.

26. Sai suka taru a kwarin Beraka, wato albarka, a rana ta huɗu, a nan suka yabi Ubangiji. Don haka har wa yau ake kiran wurin, “Kwarin Beraka.”

27. Sai kowane mutumin Yahuza da na Urushalima, tare da Yehoshafat shugabansu, suka koma Urushalima suna murna, gama Ubangiji ya sa su yi farin ciki saboda maƙiyansu.

28. Suka shigo Urushalima da molaye da garayu, da ƙaho zuwa Haikalin Ubangiji.

29. Tsoron Ubangiji kuwa ya kama dukan mulkokin ƙasashe sa'ad da suka ji Ubangiji ya yi yaƙi da maƙiyan Isra'ilawa.

30. Mulkin Yehoshafat kuwa ya sami salama, gama Allahnsa ya ba shi hutawa a kowane gefe.

31. Yehoshafat ya yi mulkin Yahuza. Yana da shekara talatin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara ashirin da biyar. Sunan tsohuwarsa Azuba, 'yar Shilhi.

32. Ya bi tafarkin tsohonsa, Asa, bai kuwa kauce ba, ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji.

33. Duk da haka ba a kawar da masujadai ba, domin har yanzu mutanen ba su tsayar da zukatansu ga Allahn kakanninsu ba.

34. Sauran ayyukan Yehoshafat, daga farko zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin tarihin Yehu ɗan Hanani, wanda aka rubuta a littafin sarakunan Isra'ila.

35. Bayan haka sai Yehoshafat, Sarkin Yahuza, ya haɗa kai da Ahaziya Sarkin Isra'ila, wanda ya aikata mugunta.

Karanta cikakken babi 2 Tar 20