Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 13:6-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Duk da haka Yerobowam ɗan Nebat, baran Sulemanu ɗan Dawuda, ya tashi, ya yi wa ɗan ubangidansa tawaye,

7. waɗansu marasa amfani, 'yan iska, suka taru suka goyi bayansa, suka raina Rehobowam ɗan Sulemanu, saboda a lokacin shi yaro ne, ba shi da ƙarfin zuciya, bai iya tsayayya da su ba.

8. Yanzu kuma, so kuke ku ƙi mulkin Ubangiji wanda yake hannun 'ya'yan Dawuda, maza, saboda yawan da kuke da shi, da gumakan maruƙan zinariya da kuke da su, waɗanda Yerobowam ya yi muku.

9. Ashe, ba ku kori firistocin Ubangiji, 'ya'yan Haruna, maza, da Lawiyawa ba, kuka yi wa kanku firistoci kamar na al'umman sauran ƙasashe? Duk wanda ya zo ya miƙa ɗan bijimi da raguna bakwai don ya tsarkake kansa, ya zama firist na gumaka ke nan, ba na Allah ba.

10. “Amma a gare mu, Ubangiji shi ne Allahnmu, ba mu kuwa rabu da shi ba. Muna da firistoci, 'ya'yan Haruna, maza, masu yi wa Ubangiji hidima, da Lawiyawa masu yi musu hidima.

11. Safe da yamma suna miƙa wa Ubangiji hadayun ƙonawa, da turare mai daɗin ƙanshi, sukan ajiye gurasar ajiyewa a kan tebur ɗin zinariya tsantsa, sukan lura da alkukin zinariya, da kuma fitilunsa kowane maraice, gama muna riƙe da umarnin Ubangiji Allahnmu, amma ku kun rabu da shi.

12. Ga shi kuwa, Allah yana tare da mu, shi ne shugabanmu, firistocinsa kuwa suna da ƙahon da akan busa lokacin yaƙi, don su busa kira na yin yaƙi. Ya ku Isra'ilawa, kada ku yi yaƙi da Ubangiji, Allah na kakanninku, gama ba za ku yi nasara ba.”

13. Ashe, Yerobowam ya riga ya sa 'yan kwanto, su yi musu yankan baya. Ƙungiyar mayaƙan Isra'ila tana fuskantar ta Yahuza, 'yan kwanto kuma suna bayansu.

14. Da Yahuza suka duba, sai ga yaƙi a gabansu da bayansu. Sai suka yi kuka ga Ubangiji, firistoci kuma suka busa ƙaho.

15. Mutanen Yahuza suka yi kūwwar yaƙi. Da suka yi kuwwar yaƙin sai Ubangiji ya sa Yerobowam da dukan jama'ar Isra'ila su gudu a gaban Abaija da Yahuza.

16. Mutanen Isra'ila kuwa suka gudu a gaban Yahuza, Allah ya bashe su a hannunsa.

17. Abaija fa, da jama'arsa suka karkashe su, mugun kisa. Mutum dubu ɗari biyar (500,000) zaɓaɓɓu na Isra'ila, aka karkashe.

Karanta cikakken babi 2 Tar 13