Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 9:4-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sai saurayin nan, annabin, ya tafi Ramot-gileyad.

5. Sa'ad da ya isa, sai ga shugabannin sojoji suna taro. Sai ya ce, “Ina da saƙo dominka, ya shugaba.”Yehu kuwa ya ce, “Wane ne a cikinmu?”Sai ya ce, “Kai ne, ya shugaba.”

6. Sai Yehu ya tashi ya shiga ɗaki, saurayin kuwa ya zuba masa mai a ka, ya ce, “Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya keɓe ka sarkin jama'arsa, wato Isra'ila.

7. Za ka hallaka gidan Ahab, maigidanka, domin in ɗau fansar jinin annabawa bayinsa, da fansar jinin sauran bayin Ubangiji a kan Yezebel.

8. Gama dukan gidan Ahab zai hallaka. Zan datse wa Ahab kowane ɗa namiji, bawa ko 'yantacce, cikin Isra'ila.

9. Zan mai da gidan Ahab kamar gidan Yeroboam ɗan Nebat, da kuma kamar gidan Ba'asha ɗan Ahija.

10. Karnuka za su cinye Yezebel a cikin Yezreyel, ba wanda zai binne ta.” Sa'an nan ya buɗe ƙofar, ya gudu.

11. Da Yehu ya fita zuwa wurin sauran shugabannin, sai suka tambaye shi, “Lafiya kuwa, me ya sa mahaukacin nan ya zo wurinka?”Sai ya ce musu, “Ai, kun san mutumin da irin maganarsa.”

12. Suka ce, “Ba mu sani ba, sai ka faɗa mana.”Shi kuwa ya ce, “Ya faɗa mini, wai Ubangiji ya ce ya keɓe ni Sarkin Isra'ila.”

13. Sai kowane mutum a cikinsu ya yi maza ya tuɓe rigarsa, ya shimfiɗa a kan matakan, sa'an nan suka busa ƙaho, suna cewa, “Yehu ne sarki.”

14. Ta haka Yehu, ɗan Yehoshafat, wato jikan Nimshi, ya tayar wa Yehoram. A lokacin, Yehoram tare da dukan Isra'ila suna tsaron Ramot-gileyad, don kada Hazayel, Sarkin Suriya, ya fāɗa mata.

15. Amma sarki Yehoram ya komo Yezreyel, don ya yi jiyyar raunukan da Suriyawa suka yi masa sa'ad da ya yi yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya. Sai Yehu ya ce, “Idan wannan shi ne nufinku, to, kada kowa ya zurare, ya tafi, ya ba da labari a Yezreyel.”

16. Sa'an nan Yehu ya hau karusarsa ya tafi Yezreyel, gama a can ne Yehoram yake kwance. Ahaziya Sarkin Yahuza ya gangara don ya gai da Yehoram.

17. Mai tsaro kuwa yana tsaye a kan hasumiya a Yezreyel, sai ya hangi rundunar Yehu sa'ad da yake zuwa. Ya ce, “Na ga wata runduna.”Sai Yehoram ya ce, “Ka aiki wani, ya hau doki, ya tafi ya tarye su, ya tambaye su, ko lafiya.”

18. Sai wani mutum ya hau doki ya tafi ya tarye su, ya ce, “Sarki ya ce, lafiya kuwa?”Sai Yehu ya ce, “Ina ruwanka da lafiya? Kewaya ka bi bayana.”Mai tsaro kuma ya ce, “Manzo ya kai wurinsu, amma bai komo ba.”

Karanta cikakken babi 2 Sar 9