Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 8:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Elisha kuwa ya ce wa matar da ya ta da ɗanta daga matattu, “Ki tashi, ke da gidanki, ki zauna duk inda kika samu, gama Ubangiji ya sa a yi yunwa a ƙasar har shekara bakwai.”

2. Sai matar ta tashi, ta yi kamar yadda annabi Elisha ya faɗa mata. Ta tafi, ita da iyalinta suka zauna a ƙasar Filistiyawa har shekara bakwai.

3. A ƙarshen shekara bakwai ɗin, matar ta komo daga ƙasar Filistiyawa, ta tafi wurin sarki, ta roƙe shi a mayar mata da gidanta da gonarta.

4. A lokacin kuwa sarki yana tare da Gehazi, wato baran annabi Elisha, ya ce, “Ka faɗa mini dukan mu'ujizan da Elisha ya yi.”

5. A sa'ad da yake faɗa wa sarki yadda Elisha ya ta da matacce, sai ga matar da ya ta da ɗanta daga matattu, ta zo ta roƙi sarki ya mayar mata da gidanta da gonarta. Sai Gehazi ya ce, “Ran sarki ya daɗe, ai, ga matar, ga kuma yaronta wanda Elisha ya tashe shi daga matattu.”

6. Da sarki ya tambayi matar sai ta faɗa masa dukan labarin. Sarki kuwa ya sa wani bafade ya mayar mata da dukan abin da yake nata da dukan amfanin gonakin, tun daga ran da ta bar ƙasar har ranar da ta komo.

7. Elisha kuwa ya tafi Dimashƙu. A lokacin kuwa Ben-hadad, Sarkin Suriya, yana ciwo. Aka faɗa masa cewa, annabi Elisha ya zo, yana nan,

8. sai sarki ya ce wa Hazayel, ɗaya daga cikin fādawansa, “Ka ɗauki kyauta, ka tafi wurin annabin Allah ka sa ya roƙar mini Ubangiji ko zan warke daga wannan cuta.”

9. Hazayel kuwa ya tafi wurin Elisha tare da kyauta iri iri na kayan Dimashƙu. Raƙuma arba'in ne suka ɗauko kayan. Da ya tafi ya tsaya a gabansa, ya ce, “Danka, Ben-hadad Sarkin Suriyawa, ya aiko ni wurinka don yana so ya ji ko zai warke daga wannan cuta.”

10. Elisha kuwa ya ce masa, “Tafi ka faɗa masa zai warke, amma Ubangiji ya nuna mini lalle zai mutu.”

11. Sai Elisha ya kafa wa Hazayel ido, yana kallonsa, har Hazayel ya ji kunya. Elisha kuwa ya fashe da kuka.

12. Hazayel ya ce, “Me ya sa shugabana yake kuka?”Elisha ya amsa ya ce, “Domin na san irin muguntar da za ka yi wa jama'ar Isra'ila. Za ka ƙone kagaransu da wuta, ka karkashe samarinsu da takobi, za ka kuma fyaffyaɗe ƙananansu a ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.”

13. Hazayel kuwa ya ce, “Ni wane ne? Ina na sami wannan iko? Ni ba kome ba ne.”Elisha ya amsa ya ce, “Ubangiji ya nuna mini za ka zama Sarkin Suriya.”

14. Sa'an nan Hazayel ya tashi daga wurin Elisha ya koma wurin Ben-hadad. Ben-hadad ya tambaye shi, “Me Elisha ya faɗa maka?”Sai ya ce, “Ya faɗa mini, cewa lalle za ka warke.”

15. Amma kashegari sai Hazayel ya ɗauki bargo, ya tsoma a ruwa, sa'an nan ya rufe fuskar sarki da shi har ya mutu.Sai ya hau gadon sarautarsa.

Karanta cikakken babi 2 Sar 8