Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Dawuda Ya Kawo Akwatin Alkawari a Urushalima

1. Dawuda kuma ya tattara zaɓaɓɓun mutane dubu talatin (30,000) na Isra'ila.

2. Sai ya tafi tare da su duka zuwa Kiriyat-yeyarim domin ya kawo akwatin Alkawarin Allah, wanda ake kira da sunan Ubangiji Mai Runduna wanda yake zaune a tsakanin kerubobin.

3-4. Suka ɗauko akwatin alkawarin Allah daga gidan Abinadab, wanda yake bisa tudu. Suka sa akwatin alkawari a sabuwar karusa. Uzza da Ahiyo, 'ya'yan Abinadeb, maza, suka bi da karusar da akwatin alkawarin Allah yake ciki. Ahiyo ne yake tafiya a gaban akwatin alkawarin.

5. Sai Dawuda da Isra'ilawa duka suka yi rawa sosai don farin ciki a gaban Ubangiji. Aka yi ta raira waƙoƙi, ana kaɗa molaye, da garayu, da goge, da kacakaura, da kuge.

6. Da suka zo masussukar Kidon, sai Uzza ya miƙa hannunsa ya riƙa akwatin alkawarin Allah, gama takarkaran sun yi kwarangyasa.

7. Ubangiji ya husata da Uzza, ya buge shi, ya mutu nan take kusa da akwatin alkawarin Allah, saboda ya taɓa akwatin alkawari.

8. Sai Dawuda ya ji haushi domin Ubangiji ya fashe haushinsa a kan Uzza. Aka sa wa wurin suna Feresauzza har wa yau.

9. Dawuda kuwa ya ji tsoron Ubangiji a ran nan, ya ce, “Ƙaƙa zan ajiye akwatin alkawarin Ubangiji a wurina?”

10. Domin haka Dawuda bai yarda ya kai akwatin alkawarin Ubangiji cikin Birnin Dawuda ba, sai ya kai shi gidan Obed-edom Bagitte.

11. Akwatin alkawarin Ubangiji yana a gidan Obed-edom Bagitte har wata uku. Ubangiji kuwa ya sa wa Obed-edom da dukan iyalinsa albarka.

An Iso da Akwatin Alkawari a cikin Urushalima

12. Aka faɗa wa Dawuda sarki, cewa, Ubangiji ya sa wa gidan Obed-edom albarka, da dukan abin da yake da shi saboda akwatin alkawarin Allah. Sai Dawuda ya tafi da murna ya kawo akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-edom zuwa Birnin Dawuda.

13. Sa'ad da masu ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji suka yi tafiya taki shida, sai Dawuda ya yi hadaya da sa, da keɓaɓɓiyar tunkiya.

14. Dawuda ya sa falmaran ta lilin. Ya kuwa yi rawa da dukan ƙarfinsa a gaban Ubangiji.

15. Shi da mutanen Isra'ila duka suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa da busar ƙaho.

16. Sa'ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal, 'yar Saul, ta leƙa ta taga, ta ga sarki Dawuda yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta raina shi a zuci.

17. Suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, suka ajiye shi a wurinsa a cikin alfarwar da Dawuda ya kafa dominsa. Dawuda ya miƙa hadayun ƙonawa da na salama a gaban Ubangiji.

18. Sa'ad da ya gama miƙa hadayun ƙonawa da na salama, sai ya sa wa mutanen albarka da sunan Ubangiji Mai Runduna.

19. Ya kuma rarraba wa dukan taron jama'ar Isra'ila, mata da maza, ƙosai, da nama, da zabibi, sa'an nan dukan mutane suka watse, kowa ya tafi gidansa.

20. Da Dawuda ya komo gida domin ya sa wa iyalinsa albarka, Mikal, 'yar Saul, ta fito domin ta tarye shi, ta ce masa, “Ƙaƙa Sarkin Isra'ila ya ɗauki kansa yau? Ya kware darajarsa a gaban barorinsa mata kamar yadda shakiyyai suke yi.”

21. Sai Dawuda ya ce wa Mikal, “Ai, na yi wannan a gaban Ubangiji wanda ya zaɓe ni a madadin mahaifinki da iyalinsa, ya naɗa ni in zama Sarkin Isra'ila, wato jama'ar Ubangiji. Lalle zan yi rawar farin ciki a gaban Ubangiji.

22. Zan mai da kaina abin raini fiye da haka, zan kuma zama abin raini gare ki, amma barori mata da kika ambata, za su girmama ni.”

23. Mikal, 'yar Saul fa, ba ta haihu ba har ta rasu.