Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Absalom ya Tayar wa Dawuda

1. Bayan wannan Absalom ya samo wa kansa karusa, da dawakai, da zagage mutum hamsin.

2. Absalom yakan tashi da wuri, ya tsaya a kan hanyar da take shiga ƙofar garin. Idan wani mai kai ƙara ya zo wurin sarki don shari'a, Absalom yakan kira shi, ya ce, “Daga ina kake?” Idan mutumin ya faɗa masa garin da ya fito daga cikin Isra'ila,

3. sai Absalom ya ce masa, “Ƙararka tana da kyau, tana kuma da gaskiya, amma sarki ba zai yi maka shari'a ba.”

4. Yakan kuma ƙara da cewa, “Kai, in da a ce ni ne alƙali a ƙasar, zan yi wa duk wanda ya zo wurina da ƙara, shari'ar gaskiya.”

5. Sa'ad da mutum ya je kusa da shi ya rusuna don ya gaishe shi, Absalom kuwa yakan rungume mutumin ya sumbace shi.

6. Haka Absalom ya riƙa yi wa dukan Isra'ilawan da suka zo wurin sarki don shari'a. Da haka ya saci zukatan mutanen Isra'ila.

7. Bayan shekara huɗu sai Absalom ya ce wa sarki, “Ina roƙonka, ka yardar mini in je Hebron in cika wa'adina wanda na yi wa Ubangiji.

8. Gama na yi wa'adi sa'ad da nake zaune a Geshur ta Suriya. Na yi wa'adi cewa, ‘Idan dai Ubangiji ya komar da ni Urushalima zan bauta masa.’ ”

9. Sarki ya ce masa, “To, ka sauka lafiya.” Sai ya tashi ya tafi Hebron.

10. Amma Absalom ya aiki manzanni a asirce cikin dukan kabilan Isra'ila a faɗa musu haka, “Da zarar kun ji an busa ƙaho, sai ku ce, ‘Absalom shi ne sarki, yana Hebron.’ ”

11. Mutum metan waɗanda ya gayyata daga Urushalima suka tafi tare da shi da zuciya ɗaya ba tare da sanin kome ba.

12. Lokacin da Absalom yake miƙa hadaya, sai ya aika zuwa Gilo a kira masa Ahitofel Bagilone mai ba Dawuda shawara. Maƙarƙashiyar kuwa ta yi ƙarfi. Mutane masu haɗa kai da Absalom suka riƙa ƙaruwa kullum.

Dawuda Ya Gudu daga Urushalima

13. Ana nan sai wani manzo ya zo wurin Dawuda, ya ce masa, “Zukatan mutanen Isra'ila suna wajen Absalom.”

14. Sa'an nan Dawuda ya ce wa fādawansa da suke tare da shi a Urushalima, “Mu tashi mu gudu, in ba haka ba ko ɗayanmu ba zai tsere daga hannun Absalom ba. Sai mu hanzarta mu gudu don kada ya tarar da mu, ya yi mana ɓarna, ya kuma kashe kowa da kowa a birnin.”

15. Fādawan suka ce, “Mu a shirye muke mu yi dukan abin da ubangijinmu sarki ya faɗa.”

16. Sarki ya fita, iyalinsa suka bi shi, amma ya bar ƙwaraƙwarai goma su lura da gidan.

17. Sarki ya fita yana tafiya da ƙafa, dukan mutane kuwa suna biye da shi. Da suka zo Bet-Merhak, wato gida na ƙarshe sai suka tsaya.

18. Dukan fādawansa, da matsaransa, wato dukan Keretiyawa, da dukan Feletiyawa, da dukan Gittiyawa, sojoji ɗari shida waɗanda suka bi Dawuda tun daga Gat suka wuce a gabansa.

19. Sarki kuwa ya ce wa Ittayi, shugabansu, “Don me kai kuma za ka tafi tare da mu? Koma ka zauna wurin sabon sarki, gama kai baƙo ne, ɗan gudun hijira kuma daga ƙasarku.

20. Jiya jiya ka zo, ba daidai ba ne in sa ka ka yi ta ragaita tare da mu, ga shi, ban san inda zan tafi ba. Koma tare da 'yan'uwanka. Ubangiji ya nuna maka alherinsa, da amincinsa.”

21. Amma Ittayi ya amsa wa sarki, ya ce, “Na rantse da zatin Ubangiji da darajar ubangijina, sarki, duk inda za ka tafi ko a mutu ko a yi rai zan tafi.”

22. Sai Dawuda ya ce masa, “To, wuce gaba.” Ittayi Bagitte kuwa ya wuce gaba tare da dukan mutanensa da 'yan yaransu.

23. Dukan ƙasar ta yi ta kururuwa sa'ad da mutane suka tashi. Sarki ya haye rafin Kidron, mutane kuma suka haye, suka nufi jeji.

24. Sai ga Abiyata ya zo, sai kuma ga Zadok ya zo tare da dukan Lawiyawa, ɗauke da akwatin alkawarin Allah. Suka ajiye akwatin har dukan mutane suka gama fita daga birnin.

25. Sa'an nan sarki ya ce wa Zadok, “Ka koma da akwatin alkawarin Allah cikin birnin. Idan na sami tagomashi a wurin Ubangiji zai komo da ni, zan sāke ganin akwatin da mazaunin zatinsa.

26. Amma idan Ubangiji bai ji daɗina ba, to, ga ni, sai ya yi yadda ya ga dama da ni.”

27. Sa'an nan sarki ya ci gaba da yi wa Zadok magana, ya ce, “Ka gani, ka koma birni lafiya, kai da Abiyata tare da 'ya'yanku biyu, wato Ahimawaz ɗanka, da Jonatan, ɗan Abiyata.

28. Ni kuwa zan dakata a nan bakin jeji har na sami labari daga gare ka.”

29. Zadok da Abiyata kuwa suka ɗauki akwatin alkawari suka koma Urushalima, suka zauna a can.

30. Dawuda yana tafe ba takalmi a ƙafarsa, ya rufe kansa, yana ta kuka, sa'ad da yake hawan Dutsen Zaitun, dukan mutane kuma da suke tare da shi suka rufe kawunansu, suna hawa, suna kuka.

31. Aka faɗa wa Dawuda cewa, “Ahitofel yana cikin 'yan maƙarƙashiya tare da Absalom.”Sai Dawuda ya yi addu'a, ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka wofintar da shawarar Ahitofel.”

32. Da Dawuda ya hau kan dutse inda ake yi wa Allah sujada, sai ga amininsa Hushai Ba'arkite, da ketacciyar riga, da ƙura a kansa, ya zo ya taryi Dawuda.

33. Dawuda kuwa ya ce masa, “Idan ka tafi tare da ni za ka zama mini nawaya.

34. Amma in za ka koma cikin birnin, ka ce wa Absalom, ‘Ya sarki, zan zama baranka kamar yadda na zama baran mahaifinka a dā. Haka zan zama baranka.’ Ta haka za ka watsar da shawarar Ahitofel.

35. Ga shi, Zadok da Abiyata, firistoci, suna tare da kai. Duk abin da ka ji daga gidan sabon sarki, sai ka faɗa wa Zadok da Abiyata, firistoci.

36. Ga 'ya'yansu biyu suna tare da su a can, wato Ahimawaz, ɗan Zadok, da Jonatan, ɗan Abiyata. Duk abin da ka ji, ka aiko su, su zo su faɗa mini.”

37. Hushai, abokin Dawuda kuwa, ya isa Urushalima daidai lokacin da Absalom yake shiga.