Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Alkawarin Allah da Dawuda

1. Sa'ad da sarki yake zaune a gidansa, Ubangiji kuma ya hutasshe shi daga fitinar abokan gābansa da suke kewaye da shi,

2. sai sarki ya ce wa annabi Natan, “Duba, ga shi, ina zaune a gidan katakon al'ul, amma akwatin alkawarin Ubangiji yana a alfarwa.”

3. Natan kuwa ya ce wa sarki, “Sai ka yi abin da yake a zuciyarka, gama Ubangiji yana tare da kai.”

4. Amma a daren nan Ubangiji ya yi magana da Natan.

5. Ya ce, “Tafi, ka faɗa wa bawana Dawuda, ka ce, in ji Ubangiji, ‘Ɗakin zama za ka gina mini?

6. Har wa yau ban taɓa zama a ɗaki ba, tun lokacin da na fito da Isra'ilawa daga Masar, amma a alfarwa nake kai da kawowa daga wannan wuri zuwa wancan.

7. A cikin kai da kawowata tare da dukan jama'ar Isra'ila ban taɓa ce wa wani daga cikin shugabannin Isra'ila waɗanda na sa su lura da jama'ata Isra'ila, ya gina mini ɗaki na katakon al'ul ba.’

8. Abin da za ka faɗa wa bawana Dawuda ke nan, in ji Ubangiji Mai Runduna, ‘Na ɗauko ka daga makiyaya inda kake kiwon tumaki domin ka zama sarkin jama'ata Isra'ila.

9. Ban kuwa rabu da kai ba duk inda ka tafi, na kuma kawar da abokan gābanka duka. Zan sa ka shahara kamar shahararrun mutane na duniya.

10-11. Zan nuna wa jama'ata Isra'ila wuri na kansu inda zan kafa su su zauna. Ba wanda zai sāke damunsu. Mugayen mutane kuma ba za su ƙara wahalshe su kamar dā ba, tun lokacin da na naɗa wa jama'ata Isra'ila mahukunta. Zan hutar da kai daga fitinar abokan gābanka duka. Banda wannan kuma ina shaida maka, cewa, zan sa gidanka ya kahu.

12. Sa'ad da kwanakinka suka ƙare, za ka rasu tare da kakanninka. A bayanka, zan ta da ɗanka, na cikinka. Zan sa mulkinsa ya kahu.

13. Shi ne zai gina mini ɗaki. Ni kuwa zan tabbatar da kursiyin sarautarsa har abada.

14. Zan zama uba gare shi, zai kuma zama ɗa a gare ni. Sa'ad da ya yi laifi zan hukunta shi da sanda kamar yadda mutane suke yi. Zan yi masa bulala kamar yadda 'yan adam suke yi.

15. Amma ba zan daina nuna masa madawwamiyar ƙaunata ba, kamar yadda na yi wa Saul wanda na kawar daga fuskata.

16. Gidanka kuwa da mulkinka za su dawwama a gabana har abada. Gadon sarautarka kuma zai kahu har abada.’ ”

17. Haka kuwa Natan ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Allah ya bayyana masa.

Addu'ar Dawuda ta Godiya

18. Sarki Dawuda ya tafi ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah, ko ni ko iyalina ba mu cancanci dukan abin da ka yi mana ba.

19. Ga shi, ka ƙara fiye da haka, ya Ubangiji Allah, gama ka yi magana, cewa, gidan bawanka zai kai kwanaki masu tsawo. Wannan ka'ida ce ta 'yan adam!

20. Me kuma zan ƙara ce maka, gama ka san bawanka, ya Ubangiji Allah.

21. Bisa ga alkawarinka da yardar zuciyarka ne ka aikata waɗannan manyan al'amura domin ka sa in san su.

22. Bisa ga dukan abin da muka ji, kai mai girma ne, ya Ubangiji Allah. Ba kamarka, in banda kai kuma babu wani Allah.

23. Ba wata al'umma kuma a duniya wadda take kama da jama'arka Isra'ila, wadda kai Allah ka fansa ta zama jama'arka. Ka mai da kanka sananne. Ka yi wa jama'arka manyan abubuwa masu banmamaki. Ka kori al'ummai da gumakansu a gaban jama'arka, waɗanda ka fansa daga Masar.

24. Ka zaɓar wa kanka jama'ar Isra'ila su zama mutanenka har abada. Kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.

25. “Ya Ubangiji Allah, yanzu ka tabbatar da maganar da ka yi da bawanka da gidansa har abada. Ka aikata bisa ga faɗarka.

26. Za a kuwa ɗaukaka sunanka da cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna shi ne Allah na Isra'ila har abada.’ Gidan bawanka Dawuda kuma zai kahu a gabanka.

27. Gama kai, ya Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, kai ne ka sanar wa ni bawanka, cewa, za ka sa gidana ya kahu, saboda haka ni bawanka na sami ƙarfin halin yin wannan addu'a a gare ka.

28. “Yanzu kuwa, ya Ubangiji Allah, kai ne Allah, kana cika alkawarinka ko yaushe. Ka kuwa yi wa bawanka alkawari mai girma.

29. Ka yarda da farin ciki ka sa wa gidan bawanka albarka domin gidansa ya dawwama a gabanka har abada, gama kai ne ka faɗa, ya Ubangiji Allah. Ka sa albarkarka ta tabbata a gidan bawanka har abada.”