Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 16:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da Dawuda ya wuce ƙwanƙolin dutsen kaɗan, sai ga Ziba baran Mefiboshet ya sadu da shi. Ya zo da jaki biyu ya yi musu labtu da gurasa dunƙule ɗari biyu, da zabibi ɗari, da sababbin 'ya'yan itace guda ɗari, da salkar ruwan inabi.

2. Sarki kuwa ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo abubuwan nan?”Ziba ya amsa, ya ce, “An kawo wa iyalin sarki jakuna su hau, da abinci, da 'ya'yan itace, domin samari su ci, ruwan inabi kuma domin waɗanda suke rafkewa a jejin su sha.”

3. Sarki kuma ya tambaye shi, “Ina ɗan ubangijinka?”Sai Ziba ya ce, “Yana zaune a Urushalima, yana cewa, ‘Yanzu dai mutanen gidan Isra'ila za su mayar mini da sarautar tsohona.’ ”

4. Da jin haka sai sarki ya ce wa Ziba, “Dukan abin da yake na Mefiboshet ya zama naka.”Ziba kuma ya rusuna ya yi godiya ya ce, “Bari in zama majidaɗin ubangijina, sarki.”

5. Sa'ad da Dawuda ya kai Bahurim, sai ga wani mutum sunansa Shimai, ɗan Gera, daga iyalin gidan Saul, ya fito yana ta zagi.

6. Ya jajjefi Dawuda da fādawansa da duwatsu, da sauran jama'a, da dukan jarumawan da suke kewaye da shi.

7. Shimai ya yi ta zagi, yana cewa, “Tafi, tafi, kai mai kisankai, sakarai.

8. Ubangiji ya sāka maka saboda alhakin jinin gidan Saul, wanda ka hau gadon sarautarsa. Yanzu Ubangiji ya ba da sarautar ga Absalom, ɗanka. Duba, masifa ta auko maka, gama kai mai kisankai ne.”

9. Sai Abishai, ɗan Zeruya, ya ce wa sarki, “Ranka ya daɗe, don me za ka bar wannan kare yana ta zaginka? Bari in tafi in fille masa kai.”

10. Amma sarki ya ce masa, “Ba ruwanku, ku 'ya'yan Zeruya. Idan yana zagi saboda Ubangiji ya sa shi, to, wa ya isa ya ce, ‘Don me kake yin haka?’ ”

11. Dawuda kuma ya ce wa Abishai da dukan fādawansa, “Ga shi ma, ɗana na cikina yana neman raina, balle wannan mutumin Biliyaminu! Ku bar shi ya yi ta zagi, gama Ubangiji ne ya umarce shi.

Karanta cikakken babi 2 Sam 16