Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 22:2-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Dawuda kuwa ya umarta a tattaro dukan baƙin da suke a ƙasar Isra'ila. Ya sa waɗansu su farfasa duwatsu, su sassaƙe duwatsun domin ginin Haikalin Allah.

3. Dawuda kuma ya cika manyan ɗakunan ajiya da ƙarafa don yin ƙusoshi na ƙyamaren ƙofofi, da mahaɗai, ya kuma tara tagulla mai yawa wanda ta fi ƙarfin awo,

4. da katakan al'ul da ba a san adadinsu ba, gama Sidoniyawa da mutanen Taya sun kawo wa Dawuda itacen al'ul mai ɗumbun yawa.

5. Dawuda kuwa ya ce, “Ɗana Sulemanu yaro ne, bai gogu da duniya ba. Ga shi, Haikalin da za a gina wa Ubangiji zai zama mai ƙayatarwa ƙwarai, zai zama sananne mai daraja cikin dukan ƙasashe, saboda haka sai in tanada masa.” Domin haka Dawuda ya tara kayayyakin gini masu ɗumbun yawa kafin rasuwarsa.

6. Sai Dawuda ya kira Sulemanu ɗansa, ya yi masa wasiyyar gina Haikalin Ubangiji, Allah na Isra'ila.

7. Dawuda kuwa ya ce wa Sulemanu, “Ɗana, na ƙudura a zuciyata in gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allah.

8. Amma Ubangiji ya ce mini, ‘Ka zubar da jini da yawa, ka yi manyan yaƙe-yaƙe, don haka ba za ka gina Haikali saboda sunana ba, gama a gabana ka zubar da jini mai yawa a duniya.

9. Za a haifa maka ɗa, zai zama mutumin salama. Zan kuwa ba shi zaman lafiya da abokan gāba da suke kewaye da shi, gama za a ce da shi Sulemanu, wato salama. Zan kawo wa Isra'ila salama, da natsuwa a zamaninsa.

10. Shi zai gina Haikali saboda sunana. Zai zama ɗana, ni kuwa zan zama uba a gare shi, zan kafa gadon sarautarsa a Isra'ila har abada.’

11. “To, ɗana, Ubangiji ya kasance tare da kai, domin ka yi nasara ka gina Haikalin Ubangiji Allahnka, kamar yadda ya faɗa a kanka.

12. Ubangiji dai ya ba ka basira da haziƙanci domin sa'ad da ya sa ka ka lura da Isra'ila ka kiyaye dokokinsa.

13. Za ka arzuta idan ka kula ka kiyaye dokoki da ka'idodi da Ubangiji ya umarci Musa saboda Isra'ila. Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karaya.

Karanta cikakken babi 1 Tar 22