Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 22:23-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Mikaiya ya ce, “Ga abin da ya faru, Ubangiji ya bar annabawanka su faɗa maka ƙarya. Amma Ubangiji kansa ya riga ya zartar maka da masifa.”

24. Sa'an nan Zadakiya ɗan Kena'ana ya matso kusa ya mari Mikaiya a fuska, ya ce, “Ƙaƙa Ruhun Ubangiji ya bar ni, ya zo ya yi magana da kai?”

25. Mikaiya ya ce masa, “A ran nan za ka gani, ka kuma gudu ka shiga har ƙurewar ɗaki don ka ɓuya.”

26. Sarki Ahab ya ce, “Ku kama Mikaiya, ku kai shi wurin Amon, shugaban birnin, da wurin Yowash ɗan sarki.

27. Ku ce musu su jefa wannan mutum a kurkuku, a riƙa ciyar da shi da abinci kaɗan da ruwan sha kaɗan, har na komo lafiya.”

28. Mikaiya kuwa ya ce, “In dai ka komo lafiya, to, Ubangiji bai yi magana da ni ba.” Ya ƙara da cewa, “Kowa ya kasa kunne ga abin da na faɗa.”

29. Ahab Sarkin Isra'ila da Sarkin Yahuza suka tafi Ramot-gileyad.

30. Sarkin Isra'ila kuwa ya ce wa Sarkin Yahuza, “Zan ɓad da kama in tafi wurin yaƙi, amma kai ka sa tufafinka na sarauta.” Sai Ahab ya ɓad da kama ya tafi wurin yaƙi.

31. Sarkin Suriya dai ya riga ya umarci shugabannin karusan yaƙinsa, su talatin da biyu, ya ce, “Kada ku yi yaƙi da kowa, kome matsayinsa, sai dai Ahab kaɗai.”

32. Sa'ad da shugabannin karusai suka ga Yehoshafat, sai suka ce, “Lalle shi ne Ahab.” Sai suka juya don su yi yaƙi da shi. Yehoshafat kuwa ya yi ihu.

33. Da shugabannin karusan yaƙi suke gane ba Ahab ba ne, sai suka rabu da shi.

34. Wani sojan Suriya kuwa ya yi sa'a, ya shilla kibiya kawai, sai ta sami Ahab, ta kafar sulkensa. Saboda haka ya ce wa mai korar karusarsa, “Ka juya, ka fitar da ni daga fagen fama gama an yi mini rauni.”

Karanta cikakken babi 1 Sar 22