Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 2:15-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Ya amsa ya ce, “Kin sani dai sarauta tawa ce. Ni ne kuwa mutanen Isra'ila duka suka sa zuciya zan ci sarautar, amma al'amarin ya sāke, sai sarautar ta zama ta ƙanena , gama tasa ce bisa ga nufin Allah.

16. Yanzu dai ina da roƙo guda zuwa gare ki, kada ki hana mini.”

17. Ta ce masa, “To, sai ka faɗa.”Sai ya ce, “In kin yarda ki yi magana da sarki Sulemanu, gama ba zai ƙi jinki ba, ki ce ya ba ni yarinyar nan, Abishag, daga Shunem, ta zama matata.”

18. Bat-sheba kuwa ta ce, “Da kyau, zan yi wa sarki magana dominka.”

19. Sa'an nan Bat-sheba ta tafi wurin sarki Sulemanu don ta yi magana da shi a kan Adonija. Sarki ya tashi domin ya tarye ta. Ya rusuna mata, sa'an nan ya zauna a kujerar sarautarsa. Ya sa aka kawo mata kujera, ta kuwa zauna a wajen damansa.

20. Sai ta ce, “Ina da wani ɗan roƙo a gare ka, kada ka hana mini shi.”Sarki ya ce mata, “Ya tsohuwata, sai ki faɗi abin da kike so, gama ba zan hana miki ba.”

21. Ta ce, “Bari a ba Adonija, ɗan'uwanka, Abishag daga Shunem, ta zama matarsa.”

22. Sai sarki Sulemanu ya amsa wa tsohuwarsa, ya ce, “Don me kika roƙar wa Adonija Abishag? Ki roƙar masa sarautar mana, gama shi wana ne, Abiyata, firist kuma, da Yowab ɗan Zeruya suna goyon bayansa.”

23. Sai sarki Sulemanu ya rantse da Ubangiji ya ce, “Allah ya kashe ni nan take idan ban sa Adonija ya biya wannan roƙo da ransa ba.

24. Ubangiji ya kafa ni sosai a gadon sarautar tsohona, Dawuda, ya kuma cika alkawarinsa, ya ba ni mulki da zuriyata. Na rantse za a kashe Adonija yau.”

25. Sai Sarki Sulemanu ya aiki Benaiya ɗan Yehoyada, ya kashe Adonija.

26. Sarki kuma ya ce wa Abiyata, firist, “Ka koma ƙasarka ta gādo a Anatot, gama ka cancanci mutuwa, amma yanzu ba zan kashe ka ba domin ka ɗauki akwatin alkawari na Ubangiji Allah a gaban Dawuda, tsohona, domin kuma ka sha wahala duka tare da tsohona.”

27. Saboda haka Sulemanu ya kori Abiyata daga aikin firist na Ubangiji, ta haka aka cika maganar da Ubangiji ya faɗa a kan gidan Eli a Shilo.

28. Da Yowab ya ji labari, gama har shi ya goyi bayan Adonija, ko da yake bai goyi bayan Absalom ba, sai ya gudu zuwa alfarwa ta Ubangiji, ya kama zankayen bagade.

29. Sa'ad da aka faɗa wa sarki Sulemanu, Yowab ya gudu zuwa alfarwa ta Ubangiji, ga shi, yana wajen bagade, sai Sulemanu ya aiki Benaiya, ɗan Yehoyada, ya je ya kashe shi.

Karanta cikakken babi 1 Sar 2