Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 8:25-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Ya ce musu, “Ina bangaskiyarku?” Suka kuwa tsorata suka yi mamaki, suna ce wa juna, “Wa ke nan kuma, har iska da ruwa ma yake yi wa umarni, suna kuwa yi masa biyayya?”

26. Sai suka iso ƙasar Garasinawa wadda take hannun riga da ƙasar Galili.

27. Da saukarsa a gaci sai wani mai aljannu ya fito daga cikin gari ya tarye shi. Ya daɗe bai sa tufa ba, ba ya zama a gida kuwa, sai a makabarta.

28. Da ganin Yesu sai ya ƙwala ihu, ya faɗi a gabansa, ya ɗaga murya ya ce, “Ina ruwanka da ni, ya Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Ina roƙonka, kada ka yi mini azaba.”

29. Ya faɗi haka ne domin Yesu ya umarci baƙin aljanin ya rabu da mutumin. Gama sau da yawa aljanin yakan buge shi, akan kuma tsare shi, a ɗaure shi da sarƙa da mari, amma ya tsintsinka ɗaurin, aljanin ya kora shi jeji.

30. Sai Yesu ya tambaye shi, “Yaya sunanka?” Ya ce, “Tuli,” don aljannu da yawa sun shiga cikinsa.

31. Sai suka yi ta roƙansa kada ya umarce su su fāɗa a mahalaka.

32. To, wurin nan kuwa akwai wani babban garkin alade na kiwo a gangaren dutse, suka roƙe shi ya yardar musu su shiga cikinsu. Ya kuwa yardar musu.

33. Sai aljannun suka rabu da mutumin, suka shiga aladun. Garken kuwa suka rungungunta ta gangaren, suka faɗa tekun, suka halaka a ruwa.

34. Da 'yan kiwon aladen nan suka ga abin da ya faru, suka gudu, suka ba da labari a birni da ƙauye.

35. Sai jama'a suka firfito su ga abin da ya auku. Suka zo wurin Yesu, suka tarar da mutumin da aljannun suka rabu da shi, zaune gaban Yesu, saye da tufa, yana cikin hankalinsa. Sai suka tsorata.

36. Waɗanda aka yi abin a idonsu kuwa, suka gaya musu yadda aka warkar da mai aljannun nan.

37. Dukan mutanen kewayen ƙasar Garasinawa suka roƙi Yesu ya rabu da su, don tsoro mai yawa ya kama su. Sai ya shiga jirgi ya koma.

38. Mutumin da aljannun suka rabu da shi kuwa, ya roƙe shi izinin tafiya tare da shi. Amma ya sallame shi ya ce,

39. “Koma gida, ka faɗi irin manyan abubuwan da Allah ya yi maka.” Sai ya tafi ko'ina a cikin birnin yana sanar da manyan abubuwan da Yesu ya yi masa.

40. To, da Yesu ya komo, taron suka yi masa maraba domin ko a dā ma duk suna jiransa ne.

41. Sai ga wani mutum mai suna Yayirus, wani shugaban majami'a, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya roƙe shi ya je gidansa.

Karanta cikakken babi Luk 8