Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 7:22-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Wanda aka kiraye shi ga tafarkin Ubangiji yana bawa, ai, 'yantacce ne na Ubangiji. Kuma, wanda aka kira shi yana ɗa, bawa ne na Almasihu.

23. Da tamani aka saye ku. Kada fa ku zama bayin mutane.

24. To, 'yan'uwa, duk halin da aka kira mutum a ciki, sai yă zauna a kai, yana zama tare da Allah.

25. A game da matan da ba su yi aure ba kuwa, ba ni da wani umarnin Ubangiji, amma ina ba da ra'ayina ne a kan ni amintacce ne, bisa ga jinƙan Ubangiji.

26. Na dai ga ya yi kyau mutum yă zauna yadda yake, saboda ƙuncin nan da yake gabatowa.

27. In da igiyar aure a wuyanka, to, kada ka nemi tsinkewa. In kuwa ba igiyar aure a wuyanka, to, kada ka nemi aure.

28. Amma kuwa in ka yi aure, ba ka yi zunubi ba, ko budurwa ma ta yi aure, ba ta yi zunubi ba. Duk da haka dai, duk masu yin aure za su ji jiki, niyyata kuwa in sawwaƙe muku.

29. Abin da nake nufi 'yan'uwa, lokacin da aka ƙayyade ya ƙure. A nan gaba masu mata su zauna kamar ba su da su,

30. masu kuka kamar ba kuka suke yi ba, masu farin ciki ma kamar ba farin ciki suke yi ba, masu saye kuma kamar ba su riƙe da kome,

31. masu moron duniya kuma, kada su ba da ƙarfi ga moronta. Don yayin duniyar nan mai shuɗewa ne.

32. Ina so ku 'yantu daga damuwa. Mutum marar aure yakan tsananta kula da sha'anin Ubangiji, yadda zai faranta wa Ubangiji rai.

33. Mutum mai aure kuwa, yakan tsananta kula da sha'anin duniya, yadda zai faranta wa matarsa rai.

34. Hankalinsa ya rabu biyu ke nan. Mace marar aure, ko budurwa, takan tsananta kula da sha'anin Ubangiji, yadda za ta kasance tsattsarka a jiki, da kuma a rai. Mace mai aure kuwa takan tsananta kula da sha'anin duniya, yadda za ta faranta wa mijinta rai.

35. Na faɗi haka ne, don in taimake ku, ba don in ƙuntata muku ba, sai dai don in kyautata zamanku, da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.

36. Ga zancen 'ya budurwa, wadda ta zarce lokacin aure, idan mahaifinta ya ga bai kyauta mata ba, in kuwa hali ya yi, sai yă yi abin da ya nufa, wato, a yi mata aure, bai yi zunubi ba.

37. In kuwa ya zamana ba lalle ne yă yi wa 'yar tasa budurwa aure ba, amma ya tsai da shawara bisa ga yadda ya nufa, ya kuma ƙudura sosai a ransa, a kan tsare ta, to, haka daidai ne.

38. Wato, wanda ya yi wa 'yar tasa budurwa aure, ya yi daidai, amma wanda bai aurar da ita ba, ya fi shi.

Karanta cikakken babi 1 Kor 7