Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rut 2:9-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ki kula da gonar da suke girbi, ki bi su. Ga shi, na riga na umarci barorina kada su dame ki. Sa'ad da kika ji ƙishirwa, sai ki tafi ki sha ruwa a tuluna, wanda barorin suka ɗebo.”

10. Sai Rut ta rusuna har ƙasa, ta ce masa, “Me ya sa na sami tagomashi a gare ka, har da za ka kula da ni, ni da nake baƙuwa?”

11. Amma Bo'aza ya ce mata, “An faɗa mini dukan abin da kika yi wa surukarki tun lokacin da mijinki ya rasu, da yadda kika bar iyayenki da ƙasarku, kika zo wurin mutanen da ba ki taɓa saninsu ba a dā.

12. Ubangiji Allah na Isra'ila, wanda kika zo neman mafaka gare shi, ya sāka miki da cikakken lada saboda abin da kika yi.”

13. Rut ta ce, “Shugaba, kā yi mini alheri ƙwarai, gama kā ta'azantar da ni, kā yi wa baiwarka maganar alheri, ko da yake ni ba ɗaya daga cikin barorinka ba ce.”

14. Da lokacin cin abinci ya yi, sai Bo'aza ya kira Rut, ya ce, “Zo nan ki ci abinci, ki riƙa tsoma lomarki a ruwan inabin da aka surka.” Sai ta zo, ta zauna kusa da masu girbin. Shi kuwa ya ba ta tumun hatsi. Ta ci, ta ƙoshi har ta bar saura.

15. Sa'ad da ta tashi, za ta yi kala, sai Bo'aza ya umarci barorinsa, ya ce, “Ku bar ta, ta yi kala a tsakanin tarin dammunan, kada ku hana ta.

16. Ku kuma riƙa zarar mata waɗansu daga dammunan don ta ɗauka, kada ku kwaɓe ta.”

17. Ta yi ta kala a gonar har yamma. Ta sussuka abin da ta kalata, ta sami tsaba wajen garwa biyu.

Karanta cikakken babi Rut 2