Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rut 2:12-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ubangiji Allah na Isra'ila, wanda kika zo neman mafaka gare shi, ya sāka miki da cikakken lada saboda abin da kika yi.”

13. Rut ta ce, “Shugaba, kā yi mini alheri ƙwarai, gama kā ta'azantar da ni, kā yi wa baiwarka maganar alheri, ko da yake ni ba ɗaya daga cikin barorinka ba ce.”

14. Da lokacin cin abinci ya yi, sai Bo'aza ya kira Rut, ya ce, “Zo nan ki ci abinci, ki riƙa tsoma lomarki a ruwan inabin da aka surka.” Sai ta zo, ta zauna kusa da masu girbin. Shi kuwa ya ba ta tumun hatsi. Ta ci, ta ƙoshi har ta bar saura.

15. Sa'ad da ta tashi, za ta yi kala, sai Bo'aza ya umarci barorinsa, ya ce, “Ku bar ta, ta yi kala a tsakanin tarin dammunan, kada ku hana ta.

16. Ku kuma riƙa zarar mata waɗansu daga dammunan don ta ɗauka, kada ku kwaɓe ta.”

17. Ta yi ta kala a gonar har yamma. Ta sussuka abin da ta kalata, ta sami tsaba wajen garwa biyu.

18. Ta ɗauka, ta koma gari, ta nuna wa surukarta abin da ta kalato. Ta kuma kawo mata sauran abincin da ta ci ta ƙoshi har ta rage.

19. Surukarta kuma ta ce mata, “A ina kika yi kala yau? A gonar wa kika yi aiki? Albarka ta tabbata ga wannan mutum wanda ya kula da ke.”Sai ta faɗa mata sunan mutumin da ta yi kala a gonarsa, ta ce, “Sunan mutumin da na yi kala a gonarsa yau, Bo'aza.”

20. Na'omi ta ce wa Rut, “Ubangiji wanda bai daina nuna alheri ga masu rai da marigayan ba, ya sa masa albarka.” Ta ƙara da cewa, “Ai, mutumin, shi danginmu ne na kusa.”

21. Rut kuma, mutuniyar Mowab, ta ce, “Banda wannan ma, ya ce mini, ‘Ki riƙa bin barorina, har lokacin da suka gama mini girbin.’ ”

22. Sa'an nan Na'omi ta ce wa Rut, “Madalla, 'yata, ki riƙa bin 'yan matan gidansa, kada ki tafi wata gona dabam.”

23. Sai ta riƙa bin 'yan matan gidan Bo'aza. Ta yi ta kala har aka gama girbin sha'ir da na alkama, tana zaune tare da surukarta, wato Na'omi.

Karanta cikakken babi Rut 2