Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mak 4:1-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ƙaƙa zinariya ta zama duhu!Ƙaƙa zinariya tsantsa ta sāke!Tsarkakakkun duwatsu kuma suna zubeA kowane magamin titi.

2. Darajar samarin SihiyonaTa kai tamanin zinariya tsantsa.To, ƙaƙa ake lissafinsu kamar tukwanen ƙasa,Aikin hannun maginin tukwane?

3. Ko diloli ma sukan ba 'ya'yansu mama,Su shayar da su.Amma mutanena sun zama kamar jiminai cikin jeji.

4. Harshen jinjiri ya liƙe a dasashinsa saboda ƙishi,'Yan yara suna roƙon abinci,Amma ba wanda ya ba su.

5. Su waɗanda suka ci abubuwa masu daɗi,Sun halaka a titi.Su waɗanda aka goye su da alharini,Yanzu suna kwance a kan tsibin toka.

6. Gama zunubin mutanenaYa fi zunubin Saduma,Wadda Ubangiji ya hallakar da ita nan da nan.

7. Keɓaɓɓunta sun fi dusar ƙanƙara tsabta,Sun kuma fi madara fari.Jikunansu sun fi murjani ja.Kyan tsarinsu yana kama da shuɗin yakutu.

8. Yanzu fuskokinsu sun fi kukunniya baƙi,Ba a iya fisshe su a titi ba,Fatar jikinsu ta liƙe wa ƙasusuwansu,Sun bushe kamar itace.

9. Gara ma waɗanda takobi ya kasheDa waɗanda yunwa ta kashe,Gama sun rame sarai saboda rashin abinci.

10. Mata masu juyayi, da hannuwansuSuka ɗauki 'ya'yansu, suka dafa,Suka zama musu abinci a lokacin halakar mutanena.

11. Ubangiji ya saki fushinsa,Ya zuba fushinsa mai zafi.Ya kunna wa Sihiyona wutaWadda ta cinye harsashin gininta.

12. Sarakunan duniya da mazaunanta ba su gaskata,Cewa abokan gaba ko maƙiyaZa su iya shiga ƙofofin Urushalima ba.

13. Dalili kuwa saboda zunuban annabawa ne,Da muguntar firistoci,Waɗanda suka kashe adalai.

14. Sun yi ta kai da kawowa a titi kamar makafi,Sun ƙazantu da jiniHar ba wanda zai taɓa rigunansu.

15. Mutane suka yi ta yi musu ihu,Suna cewa, “Ku tafi, ku ƙazamai,Ku tafi, ku tafi, kada ku taɓa mu!”Don haka suka zama korarru, masu kai da kawowa.A cikin sauran al'umma mutane suna cewa,“Ba za su ƙara zama tare da mu ba.”

16. Ubangiji kansa ya watsar da su,Ba zai ƙara kulawa da su ba.Ba su darajanta firistoci ba,Ba su kuma kula da dattawa ba.

17. Idanunmu sun gajiDa zuba ido a banza don samun taimako,Mun zuba idoGa al'ummar da ba za ta iya cetonmu ba.

18. Ana bin sawayenmu,Don haka ba mu iya tafiya a titunanmu ba.Ƙarshenmu ya yi kusa,Kwanakinmu sun ƙare,Gama ƙarshenmu ya zo.

Karanta cikakken babi Mak 4