Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 31:15-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Ubangiji kuwa ya bayyana a cikin alfarwar a al'amudin girgije. Al'amudin girgijen kuwa ya tsaya a ƙofar alfarwar.

16. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ga shi, za ka rasu ka tarar da kakanninka. Wannan jama'a kuwa za ta fara kaucewa daga hanya, su bi gumakan ƙasar da za su shiga, su zauna. Za su rabu da ni, su ta da alkawarina wanda na yi da su.

17. A wannan rana zan husata da su ƙwarai, in rabu da su, in ɓoye musu fuskata, za a cinye su. Masifu da wahalai za su same su. Za su kuwa ce a ranar, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu.’

18. Hakika kuwa, zan ɓoye musu fuskata sabili da muguntar da suka aikata, suka kuma bi gumaka.

19. “Don haka, sai ka rubuta wannan waƙa, ka koya wa Isra'ilawa. Ka sa ta a bakinsu don waƙan nan ta zama shaida a gare ni game da Isra'ilawa.

20. Sa'ad da na kawo su a ƙasar da take da yalwar abinci, wadda na rantse zan ba kakanninsu, har suka ci, suka ƙoshi, suka yi ƙiba, za su juya, su bi gumaka, su bauta musu. Za su raina ni, su tā da alkawarina.

21. Sa'ad da yawan masifun nan da wahalan nan suka same su, to, waƙar nan za ta ba da shaida a kansu, gama zuriyarsu ba za ta manta da wannan waƙa ba, gama na san ƙudurin da suke yi kafin in kawo su ƙasar da na rantse zan bayar.”

22. Saboda wannan sai Musa ya rubuta wannan waƙa a ranar, ya koya wa jama'ar Isra'ila.

Karanta cikakken babi M. Sh 31