Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 9:19-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Yanzu dai idan abin da kuka yi wa Yerubba'al da iyalinsa daidai ne, to, sai ku yi farin ciki da Abimelek, ku sa shi kuma ya ji daɗinku.

20. Amma idan ba haka yake ba, Allah ya sa wuta ta fito daga wurin Abimelek ta cinye mutanen Shekem da na Bet-millo. Bari Allah ya sa kuma wuta ta fito daga wurin mutanen Shekem da na Bet-millo ta cinye Abimelek.”

21. Sa'an nan Yotam ya tsere. Ya tafi ya zauna a Biyer, gama yana tsoron ɗan'uwansa Abimelek.

22. Abimelek kuwa ya yi shekara uku, yana mulkin Isra'ila.

23. Ubangiji kuma ya sa husuma ta tashi tsakanin Abimelek da mutanen Shekem. Shugabannin Shekem kuwa suka tayar masa.

24. Wannan ya faru domin a ɗauki fansar jinin, 'ya'yan Yerubba'al, maza, su saba'in, a kan Abimelek ɗan'uwansu, wanda ya kashe su, da kuma a kan shugabannin Shekem, waɗanda suka taimake shi ya kashe 'yan'uwansa.

25. Shugabannin Shekem kuwa suka sa mutane su yi kwanto a kan dutwatsu gāba da Abimelek. Suka yi wa duk wanda ya bi ta wannan hanya fashi. Sai aka faɗa wa Abimelek.

26. Ga'al, ɗan Ebed, da 'yan'uwansa suka yi ƙaura zuwa Shekem. Shugabannin Shekem kuwa suka amince da shi.

27. Suka tafi gona, suka ɗebo inabi, suka matse, suka yi biki a gidan gunkinsu. Suka ci, suka sha, suka zazzagi Abimelek.

28. Ga'al, ɗan Ebed, ya ce, “Wane ne Abimelek har mu mutanen Shekem za mu bauta masa? Ashe, ba Yerubba'al ne mahaifinsa ba, Zebul kuma shugaban yaƙinsa? Don me za mu bauta masa? Ku yi aminci ga kakanku Hamor, tushen kabilarku!

29. Da ma a ce nake shugabancin mutanen nan, da sai in hamɓare Abimelek!” Sai ya ce wa Abimelek, “Ka tara yawan rundunarka ka fito.”

30. Zebul, shugaban birnin ya ji maganganun Ga'al, ɗan Ebed, sai ya husata.

31. Ya aiki jakadu wurin Abimelek a Aruma, ya ce, “Ga fa Ga'al, ɗan Ebed, da 'yan'uwansa sun zo Shekem, suna kutta garin ya tayar maka.

Karanta cikakken babi L. Mah 9