Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 9:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Abimelek, ɗan Yerubba'al, wato Gidiyon, ya tafi Shekem wurin dukan dangin mahaifiyarsa, ya ce musu,

2. “Ina roƙonku, ku yi magana da shugabannin Shekem, ku ce, ‘Me ya fi muku kyau, 'ya'yan Yerubba'al, maza saba'in su yi mulkinku, ko kuwa mutum ɗaya ya yi mulkinku?’ Amma ku tuna fa ni jininku ne.”

3. Sai dangin mahaifiyarsa suka yi magana da shugabannin Shekem saboda shi. Zuciyarsu kuwa ta saje da Abimelek, gama suka ce, “Shi ɗan'uwanmu ne.”

4. Suka kuma ba shi azurfa saba'in daga cikin gidan gunkin nan Ba'al-berit. Da wannan azurfa Abimelek ya yi ijarar 'yan iska waɗanda suka bi shi.

5. Ya tafi gidan mahaifinsa a Ofra, ya kashe 'yan'uwansa maza, wato 'ya'yan Yerubba'al, mutum saba'in a kan dutse guda. Amma Yotam ƙaramin ɗan Yerubba'al, shi kaɗai ya ragu domin ya ɓuya.

6. Sai shugabannin Shekem duka da na Betmillo suka taru suka naɗa Abimelek sarki kusa da itacen oak na al'amudin da yake a Shekem.

7. Da Yotam ya ji wannan sai ya tafi, ya tsaya a kan Dutsen Gerizim, da babbar murya, ya ce musu, “Ku kasa kunne gare ni ku mutanen Shekem, domin kuma Allah ya kasa kunne gare ku!

8. Wata rana itatuwa suka taru don su naɗa wa kansu sarki. Suka ce wa itacen zaitun, ‘Kai ka zama sarkinmu.’

9. Amma itacen zaitun ya ce musu, ‘In bar maina wanda da shi ake girmama alloli da mutane, don in tafi in yi ta fama da itatuwa?’

10. Sai kuma itatuwa suka ce wa itacen ɓaure, ‘Ka zo, ka zama sarkinmu.’

11. Amma itacen ɓaure ya ce musu, ‘In bar kyawawan 'ya'yana masu zaƙi, don in tafi in yi ta fama da itatuwa?’

12. Itatuwa kuma suka ce wa kurangar inabi, ‘Ki zo, ki mallake mu.’

13. Sai kurangar inabi ta ce, ‘In bar ruwan inabina wanda yake faranta zuciyar allolin da ta mutane, don in tafi, in yi ta fama da itatuwa?’

14. Sa'an nan dukan itatuwa suka ce wa itacen ƙaya, ‘Ka zo, ka zama sarkinmu.’

15. Itacen ƙaya kuwa ya ce wa itatuwan, ‘In da gaske kuke, kuna so ku naɗa ni sarkinku, to, sai ku zo, ku fake a inuwata, in ba haka ba kuwa, bari wuta ta fito daga itacen ƙaya ta cinye itacen al'ul na Lebanon.’ ”

Karanta cikakken babi L. Mah 9