Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 4:10-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sai su sa alkukin da dukan kayayyakinsa a cikin fatar awaki su naɗe, su sarƙafa shi asandan ɗaukarsa.

11. A rufe bagaden zinariya da shuɗin zane, a kuma rufe shi da fatun awaki, sa'an nan a zura sandunan ɗaukarsa.

12. Su ɗauki dukan kwanonin da ake amfani da su a Wuri Mai Tsarki, su sa su cikin shuɗin zane, sa'an nan su rufe su da fatun awaki, a sarƙafa su a sanda don a ɗauka.

13. Za su kwashe tokar da take cikin bagaden, su rufe bagaden da shunayyan zane.

14. Sa'an nan su sa dukan kayayyakin bagaden a kansa waɗanda ake aiki da su a wurin, wato su farantai don wuta, da cokula masu yatsotsi, da manyan cokula, da daruna da dai dukan kayayyakin bagaden. Su kuma rufe bagaden da fatun awaki, sa'an nan su zura sandunan ɗaukarsa.

15. Sa'ad da Haruna da 'ya'yansa maza suka gama kintsa Wuri Mai Tsarki da kayayyakinsa duka a lokacin tashi, sai 'ya'yan Kohat, maza, su zo su ɗauke kayayyakin, amma kada su taɓa abubuwan nan masu tsarki domin kada su mutu.Waɗannan su ne ayyukan 'ya'yan Kohat a duk lokacin da za a naɗe alfarwa ta sujada.

16. Ele'azara kuwa, ɗan Haruna, firist, shi ne zai lura da man fitila, da turare, da hadayar gari ta kullum, da man keɓewa, ya kuma kula da dukan alfarwar, da duk abin da yake cikinta, da Wuri Mai Tsarki, da kayayyakinsa.

17. Sai Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

18. “Kada ku bar zuriyar Kohat

19. ta hallaka ta wurin kusatar waɗannan tsarkakakkun abubuwa. Maganin abin, shi ne sai Haruna da 'ya'yansa maza, su shiga, su nuna wa kowannensu irin aikin da zai yi, da kayan da zai ɗauka.

20. Amma idan Kohatawa suka shiga alfarwar suka tarar firistoci suna shisshirya tsarkakakkun abubuwa don tashi, har dai in sun gani, to za su mutu.”

21. Ubangiji ya kuma faɗa wa Musa,

22. ya ƙidaya 'ya'yan Gershon, maza, bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu

23. ya rubuta su tun daga mai shekara talatin, har zuwa mai shekara hamsin, duk wanda ya isa yin aikin da zai yi a alfarwa ta sujada.

24. Wannan shi ne aikin da iyalan Gershonawa za su yi wajen ɗaukar kaya.

25. Za su ɗauki alfarwa ta sujada, da labule na ciki da na waje, da murfi na fatun tumaki wanda yake a bisa alfarwar, da kuma labulen ƙofar alfarwa ta sujada,

26. da labulen farfajiya, da labulen ƙofar farfajiya wadda ta kewaye alfarwar da bagaden, da igiyoyinsu, da duk kayayyakinsu na yin aiki. Sai su yi dukan abin da ya kamata a yi da su.

27. Haruna ne da 'ya'yansa maza za su nuna wa 'ya'yan Gershonawa irin aikin da za su yi, da kayayyakin da za su ɗauka. Sai a faɗa musu dukan abin da za su yi, da dukan abinda za su ɗauka.

Karanta cikakken babi L. Kid 4