Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 14:7-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Suka ce wa dukan taron jama'ar Isra'ilawa, “Ƙasar da muka ratsa ta don mu leƙi asirinta, ƙasa ce mai kyau ƙwarai da gaske.

8. Idan Ubangiji yana jin daɗinmu zai kai mu a wannan ƙasa da take cike da yalwar abinci, ya ba mu ita.

9. Sai dai kada ku tayar wa Ubangiji, kada kuwa ku ji tsoron mutanen ƙasar. Za mu ci su ba wuya, Ubangiji kuma zai lalatar da gumakansu da suke kāre su. Ubangiji kuwa yana tare da mu, kada ku ji tsoronsu.”

10. Amma taron jama'a suka ce za su jajjefe su da duwatsu. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan mutanen Isra'ila daga cikin alfarwa ta sujada.

11. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe mutanen nan za su raina ni? Har yaushe za su ƙi gaskata ni, ko da yake na aikata alamu a tsakiyarsu?

12. Zan kashe su da annoba, in raba su da gādonsu. Zan yi wata al'umma da kai, wadda za ta fi su girma da iko.”

13. Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ai, Masarawa za su ji, gama ka fitar da mutanen daga cikinsu da ƙarfin ikonka.

14. Za su kuwa faɗa wa mutanen wannan ƙasa, gama sun riga sun ji, kai, ya Ubangiji, kana cikin tsakiyar jama'ar nan wadda kake bayyana kanka gare ta fuska da fuska. Girgijenka kuma yana tsaye a kansu, kakan kuma yi musu jagora da al'amudin wuta.

15. Idan kuwa ka kashe jama'ar nan gaba ɗaya, sai al'umman da suka ji labarinka, su ce,

16. ‘Domin Ubangiji ya kāsa kai jama'ar nan zuwa cikin ƙasar da ya rantse zai ba su, don haka ya kashe su a cikin jeji.’

17. Yanzu fa, ya Ubangiji, ina roƙonka ka sa ikonka ya zama da girma kamar yadda ka alkawarta cewa,

18. ‘Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai yawan ƙauna, kana gafarta mugunta da laifi, amma ba za ka ƙyale mai laifi ba, gama kakan ɗora wa 'ya'ya alhakin muguntar iyaye, har tsara ta uku da ta huɗu.’

19. Ina roƙonka ka gafarta muguntar wannan jama'a saboda ƙaunarka mai girma, kamar yadda kake gafarta musu tun daga Masar har zuwa yanzu.”

Karanta cikakken babi L. Kid 14