Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

An Keɓe Biranen Mafaka

1. Sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa,

2. “Ka faɗa wa jama'ar Isra'ila, su keɓe biranen mafaka waɗanda na faɗa wa Musa ya faɗa muku.

3. Domin idan wani mutum ya yi kisankai ba da niyya ba, ba kuma da saninsa ba, sai ya tsere zuwa can. Biranen za su zama muku mafaka daga mai bin hakkin jini.

4. Wanda ya yi kisankan sai ya tsere zuwa ɗaya daga cikin biranen, ya tsaya a bakin ƙofar birnin, ya bayyana wa dattawan garin abin da ya same shi. In sun ji, sai su shigar da shi a birnin, su ba shi wurin zama, ya zauna tare da su.

5. Idan mai bin hakkin jinin ya bi shi, ba za su ba shi wanda ya yi kisankan ba, domin bai kashe maƙwabcinsa da gangan ba, ba kuma ƙiyayya a tsakaninsu dā ma.

6. Zai yi zamansa a birnin har lokacin da aka gabatar da shi gaban dattawa don shari'a, sai kuma bayan rasuwar babban firist na lokacin, sa'an nan wanda ya yi kisankan zai iya komawa garinsu da gidansa daga inda ya tsere.”

7. Saboda haka suka keɓe Kedesh ta Galili a ƙasar tuddai ta Naftali, da Shekem ta ƙasar tuddai ta Ifraimu, da Kiriyat-arba, wato Hebron, ta ƙasar tuddai ta Yahuza.

8. A hayin Urdun, gabas da Yariko, suka keɓe Bezer ta jeji a kan tudu a cikin yankin kabilar Ra'ubainu, da Ramot cikin Gileyad ta kabilar Gad, da Golan cikin Bashan ta kabilar Manassa.

9. Waɗannan su ne biranen mafaka da aka keɓe domin dukan Isra'ilawa, da baƙin da suke baƙuntaka cikinsu. Don duk wanda ya yi kisankai ba da niyya ba zai iya tserewa zuwa can don kada ya mutu ta hannun mai bin hakkin jini. Zai zauna a can har lokacin da za a gabatar da shi a gaban taron jama'a.