Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Yankin Ƙasar da Aka Ba Yahuza

1. Rabon da aka ba jama'ar Yahuza bisa ga iyalansu ya yi kudu, a iyakar Edom zuwa jejin Zin, can kudu nesa.

2. Iyakarsu wajen kudu ta miƙa tun daga ƙarshen Tekun Gishiri, daga wajen gaɓar da ta fuskanci kudu.

3. Ta milla kudanci hawan Akrabbim, ta zarce zuwa Zin, ta haura kudu da Kadesh-barneya, ta wajen Hesruna har zuwa Addar. Sai ta karkata zuwa Karka.

4. Ta zarce zuwa Azemon, ta bi ta rafin Masar zuwa inda ya gangara a teku. Wannan ita ce iyakar mutanen Yahuza wajen kudu.

5. Iyakarsu wajen gabas ta kama daga Tekun Gishiri zuwa bakin Urdun. Wajen arewa kuwa ta miƙa daga bakin teku a inda Kogin Urdun ya gangara a tekun.

6. Iyakar ta bi zuwa Bet-hogla, ta zarce zuwa arewa da Bet-araba, ta haura zuwa Dutsen Bohan, ɗan Ra'ubainu.

7. Daga kwarin Akor ta wuce zuwa Debir ta yi wajen arewa, sa'an nan ta juya zuwa Gilgal wadda take daura da hawan Adummim wanda yake kudancin gefen kwarin. Sai ta zarce zuwa ruwan En-shemesh, ta ƙare a En-rogel.

8. Daga nan iyakar ta bi ta kwarin ɗan Hinnom a wajen kudancin kafaɗar Yebus, wato Urushalima. Ta kuwa bi ta dutsen da yake shimfiɗe daura da kwarin Hinnom wajen yamma, a arewacin ƙarshen kwarin Refayawa.

9. Ta kuma milla daga kan dutsen zuwa maɓuɓɓugar ruwan Neftowa, daga can zuwa biranen Dutsen Efron. Daga can kuma ta karkata zuwa Ba'ala, wato Kiriyat-yeyarim.

10. Ta kuma kewaye kudancin Ba'ala zuwa Dutsen Seyir. Ta zarce zuwa arewacin kafaɗar Dutsen Yeyarim, wato Kesalon. Daga nan ta gangara zuwa Bet-shemesh, ta kuma wuce zuwa Timna.

11. Iyakar kuma ta biya wajen kafaɗar tudun, arewa da Ekron, sa'an nan ta karkata zuwa Shikkeron, ta wuce zuwa Dutsen Ba'ala, ta tafi zuwa Yabneyel, sa'an nan ta gangara a teku.

12. Bakin Bahar Rum, ita ce iyaka a wajen yamma. Wannan ita ce iyakar da ta kewaye jama'ar Yahuza bisa ga iyalansu.

Kalibu Ya Ci Hebron da Debir da Yaƙi

13. Kamar yadda Ubangiji ya umarci Joshuwa, ya ba Kalibu, ɗan Yefunne, rabonsa a tsakiyar jama'ar Yahuza. Rabon da aka ba shi, shi ne Kiriyat-arba, wato Hebron. Arba shi ne uban Anak.

14. Daga can sai Kalibu ya kori 'ya'yan Anak, maza, su uku, da Sheshai, da Ahiman, da Talmai, zuriyar Anak.

15. Daga can kuma ya tafi ya fāɗa wa mazaunan Debir, dā sunan Debir Kiriyat-sefer ne.

16. Kalibu ya ce, “Duk wanda ya bugi Kiriyat-sefer, har ya ci ta, zan ba shi 'yata Aksa aure.”

17. Otniyel kuwa, ɗan Kenaz, ɗan'uwan Kalibu, ya ci Kiriyat-sefer. Kalibu kuwa ya ba shi Aksa 'yarsa aure.

18. Da ta zo wurinsa, ya zuga ta ta roƙi mahaifinta saura. Da ta sauka daga kan jakinta, sai Kalibu ya ce mata, “Me kike so?”

19. Ta kuwa ce masa, “Ka yi mini alheri, da yake ka tura ni a ƙasar Negeb, ina roƙonka ka ba ni maɓuɓɓugar ruwa.” Kalibu kuwa ya ba ta maɓuɓɓugar tuddai da na kwari.

Biranen Kabilar Yahuza

20. Wannan shi ne gādon jama'ar Yahuza bisa ga iyalansu.

21. Biranen jama'ar Yahuza da suke can kudu sosai wajen iyakar Edom, su ne Kabzeyel, da Eder, da Yagur,

22. da Kina, da Dimona, da Adada,

23. da Kedesh, da Hazor, da Yitnan,

24. da Zif, da Telem, da Beyalot,

25. da Hazor-hadatta, da Kiriyot-hesruna, wato Hazor,

26. da Amam, da Shema, da Molada,

27. da Hazar-gadda, da Heshmon, da Bet-felet,

28. da Hazar-shuwal, da Biyer-sheba, da Biziyotaya,

29. da Ba'ala, da Abarim, da Ezem,

30. da Eltola, da Kesil, da Horma,

31. da Ziklag, da Madmanna, da Sansanna,

32. da Labayot, da Shilhim, da Ayin, da Rimmon. Birane ashirin da tara ke nan da ƙauyukansu.

33. Na filayen kwarin kuwa, su ne Eshtawol, da Zora, da Ashna,

34. da Zanowa, da En-ganim, da Taffuwa, da Enayim,

35. da Yarmut, da Adullam, da Soko, da Azeka,

36. da Shayarim, da Aditayim, da Gedera, da Gederotayim. Birane goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu.

37. Da kuma Zenan, da Hadasha, da Migdal-gad,

38. da Dileyan, da Mizfa, da Yokteyel,

39. da Lakish, da Bozkat, da Eglon,

40. da Kabbon, da Lahmam, da Kitlish,

41. da Gederot, da Bet-dagon, da Na'ama, da Makkeda, birane goma sha shida ke nan da ƙauyukansu.

42. Da kuma Libna, da Eter, da Ashan,

43. da Yifta, da Ashna, da Nezib,

44. da Kaila, da Akzib, da Maresha, birane tara ke nan da ƙauyukansu.

45. Da kuma Ekron da garuruwanta da ƙauyukanta.

46. Daga Ekron zuwa tekun, da dukan garuruwa da ƙauyukan da suke kusa da Ashdod.

47. Ashdod da garuruwanta da ƙauyukanta, Gaza da garuruwanta da ƙauyukanta zuwa rafin Masar da Bahar Rum da bakinta.

48. Birane na cikin ƙasar tuddai kuwa, su ne Shamir, da Yattir, da Soko,

49. da Danna, da Kiriyat-sanna, wato Debir,

50. da Anab, da Eshtemowa, da Anim,

51. da Goshen, da Holon, da Gilo. Birane goma sha ɗaya ke nan da ƙauyukansu.

52. Da kuma Arab, da Duma, da Eshan,

53. da Yanim, da Bet-taffuwa, da Afeka,

54. da Hunta, da Kiriyat-arba, wato Hebron, da Ziyor, birane tara ke nan da ƙauyukansu.

55. Da kuma Mawon, da Karmel, da Zif, da Yutta,

56. da Yezreyel, da Yokdeyam, da Zanowa,

57. da Kayin, da Gebeya, da Timna, birane goma ke nan da ƙauyukansu.

58. Halhul, da Bet-zur, da Gedor,

59. da Ma'arat, da Bet-anot da Eltekon, birane shida ke nan da ƙauyukansu.

60. Da kuma Kiriyat-ba'al, wato Kiriyat-yeyarim, da Rabba, birane biyu ke nan da ƙauyukansu.

61. Biranen da suke a jeji kuwa su ne Bet-araba, da Middin, da Sekaka,

62. da Nibshan, da Birnin Gishiri, da En-gedi, birane shida ke nan da ƙauyukansu.

63. Amma jama'ar Yahuza ba su iya korar Yebusiyawa waɗanda suke zaune a Urushalima ba, don haka Yebusiyawa suka yi zamansu da jama'ar Yahuza cikin Urushalima har wa yau.