Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Saminu

1. Kuri'a ta biyu ta faɗa kan kabilar Saminu bisa ga iyalanta. Nasu rabon gādon yana tsakiyar rabon gādon kabilar Yahuza.

2. Waɗannan su ne wuraren da suka gāda, Biyer-sheba, da Sheba, da Molada,

3. da Hazar-shuwal, da Bilha, da Ezem,

4. da Eltola, da Betul, da Horma,

5. da Ziklag, da Bet-markabot, da Hazar-susa,

6. da Bet-lebawot, da Sharuhen. Garuruwa goma sha uku ke nan da ƙauyukansu.

7. Akwai kuma Ayin, da Rimmon, da Eter, da Ashan. Garuruwa huɗu ke nan da ƙauyukansu,

8. da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da waɗannan garuruwa tun daga Ba'alat-biyer, wato Ramot ta Negeb. Wannan shi ne rabon gādon iyalan kabilar Saminu.

9. Gādon kabilar Saminu yana cikin yankin ƙasar rabon kabilar Yahuza domin rabon kabilar Yahuza ya yi mata yawa, don haka kabilar Saminu ta sami gādo daga cikin tsakiyar gādon kabilar Yahuza.

Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Zabaluna

10. Kuri'a ta uku ta faɗa a kan kabilar Zabaluna bisa ga iyalanta. Yankin ƙasar gādonsu ya kai har Sarid.

11. Iyakar ta hau wajen yamma zuwa Marala, ta kai Dabbeshet da rafin da yake gabas da Yakneyam.

12. Daga Sarid, ta nufi wajen gabas zuwa iyakar Kislotabar, sa'an nan ta bi ta Daberat da Yafiya.

13. Daga can ta miƙa wajen gabas zuwa Gat-hefer da Et-kazin, har zuwa Rimmon inda ta nausa zuwa Neya.

14. Daga wajen arewa iyakar ta juya zuwa Hannaton, sa'an nan ta faɗa a kwarin Iftahel.

15. Waɗannan garuruwa, da Kattat, da Nahalal, da Shimron, da Idala, da Baitalami, suna cikin garuruwa goma sha biyu da ƙauyukansu da suke cikin yankin ƙasar kabilar Zabaluna.

16. Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke cikin gādon mutanen Zabaluna bisa ga iyalansu.

Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Issaka

17. Kuri'a ta huɗu ta faɗo a kan kabilar Issaka bisa ga iyalanta.

18. Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar su ne, Yezreyel, da Kesullot, da Shunem,

19. da Hafarayim, da Shiyon, da Anaharat,

20. da Rabbit, da Kishiyon, da Ebez,

21. da Remet da En-ganim, da En-hadda, da Bet-fazzez.

22. Iyakar kuma ta bi ta Tabor, da Shahazuma, da Bet-shemesh. Sa'an nan ta gangara a Kogin Urdun. Akwai garuruwa goma sha shida da ƙauyukansu.

23. Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke a yankin ƙasar da kabilar Issaka ta gāda bisa ga iyalanta.

Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Ashiru

24. Kuri'a ta biyar ta fāɗo a kan kabilar Ashiru bisa ga iyalanta.

25. Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar, su ne Helkat, da Hali, da Beten, da Akshaf,

26. da Alammelek, da Amad, da Mishal. A wajen yamma, iyakar ta bi ta Karmel da Shihor-libnat.

27. Daga nan sai ta nausa wajen gabas, ta bi ta Bet-dagon, da Zabaluna, da kwarin Iftahel a wajen arewa zuwa Bet-emek da Nayil. Ta yi gaba a wajen arewa zuwa Kabul,

28. da Hebron, da Rehob, da Hammon, da Kana, har ta bi ta Sidon Babba.

29. Daga can ta nausa zuwa Rama, ta bi ta garun birnin Taya, sai kuma ta nausa zuwa Hosa, sa'an nan ta gangara Bahar Rum, wajen Mahalab, da Akzib,

30. da Umma, da Afek, da Rehob. Garuruwa ashirin da biyu ke nan da ƙauyukansu.

31. Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke cikin yankin ƙasar da kabilar Ashiru ta gāda bisa ga iyalanta.

Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Naftali

32. Kuri'a ta shida ta faɗo a kan kabilar Naftali bisa ga iyalanta.

33. Tasu iyaka, ta miƙa daga Helef, daga itacen oak da yake cikin Za'anannim, da Adami-nekeb, da Yabneyel har zuwa Lakkum, sa'an nan ta tsaya a Kogin Urdun.

34. Iyakar kuma ta juya wajen kudu zuwa Aznot-tabor, daga can ta miƙa zuwa Hukkok, sa'an nan ta kai Zabaluna wajen kudu, da Ashiru wajen yamma, da Yahuza wajen gabas wajen Urdun.

35. Garuruwan da yake da garu su ne, Ziddim, da Zer, da Hammat, da Rakkat, da Kinneret,

36. da Adama, da Rama, da Hazor,

37. da Kedesh, da Edirai, da En-hazor,

38. da Iron, da Migdal-el, da Horem, da Bet-anat, da Bet-shemesh. Garuruwa goma sha tara ke nan da ƙauyukansu.

39. Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon gādon kabilar Naftali da iyalanta.

Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Dan

40. Kuri'a ta bakwai ta faɗo a kan kabilar Dan bisa ga iyalanta.

41. Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar gādonta ke nan, da Zora, da Eshtawol, da Ir-shemesh,

42. da Shalim, da Ayalon, da Itla,

43. da Elon, da Timna, da Ekron,

44. da Elteki, da Gebbeton, da Ba'alat,

45. da Yahud, da Bene-berak, da Gat-rimmon,

46. da Meyarkon, da Rakkon, tare da karkarar da take gefen Yaffa.

47. Sa'ad da Danawa suka rasa karkararsu, suka tafi, suka yaƙi Leshem. Da suka ci ta, sai suka hallaka mutanenta da takobi, suka mallaki ƙasar, suka zauna a ciki. Suka kuma sa wa Leshem, sunan kakansu, wato Dan.

48. Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon kabilar Dan bisa ga iyalanta.

Yankin Ƙasar da aka Ba Joshuwa

49. Sa'ad da mutanen Isra'ila suka gama rarraba gādon ƙasar, suka ba Joshuwa ɗan Nun nasa rabo a cikin nasu.

50. Bisa ga umarnin Ubangiji, suka ba shi garin da ya roƙa, wato Timnatsera a ƙasar tudu ta Ifraimu. Ya sāke gina garin, ya kuwa zauna a ciki.

51. Waɗannan su ne rabe-raben gādon da Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin kakannin gidajen kabilan jama'ar Isra'ila, suka rarraba ta hanyar jefa kuri'a a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada a Shilo. Ta haka suka gama rarraba ƙasar.