Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 44:19-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Masu ƙera gumaka ba su da ko tunanin da za su ce, “Na ƙone wani sashi na itacen nan. Na toya gurasa a garwashin, na kuma gasa nama, na ci shi, na kuwa ce sauran itacen zan sassaƙa gunki da shi. Ga ni yanzu, ina ta rusunawa gaban guntun itace!”

20. Ya zama daidai kamar mutum ya ci toka. Manufarsa ta wauta ta ɓatar da shi, har ba yadda za a iya taimakonsa. Ba zai iya ganewa ba, gunkin da ya riƙe a hannunsa ba allah ba ne ko kaɗan.

21. Ubangiji ya ce,“Ka tuna da waɗannan abu, ya Isra'ila,Ka tuna kai bawana ne.Na halicce ka domin ka zama bawana,Ba zan taɓa mantawa da kai ba.

22. Na shafe zunubanka kamar baƙin girgije,Da girgije kuma zan rufe laifofinkaKa komo wurina, ni ne na fanshe ka.”

23. Ku yi sowa ta farin ciki ya ku sammai!Ku yi sowa ku zurfafan wurare na duniya!Ku yi sowa ta murna, ku duwatsu, da kowane itace na jeji!Ubangiji ya fanshi mutanensa, Isra'ila,Saboda haka ya nuna girmansa.

24. “Ni ne Ubangiji, Mahaliccinku, Mai Fansarku.Ni ne Ubangiji, Mahaliccin dukkan abu.Ni kaɗai na shimfiɗa sammai,Ba wanda ya taimake ni sa'ad da na yi duniya.

25. Na sa masu duba su zama wawaye,Na sassāke annabce-annabcen masanan taurari.Na bayyana kuskuren maganar masu hikima,Na kuma nuna masu hikimarsu wauta ce.

26. Amma sa'ad da bawana ya yi annabci,Sa'ad da na aika da manzona domin ya bayyana shirye-shiryena,Na sa waɗannan shirye-shirye da annabce-annabce su cika.Ina faɗa wa Urushalima, cewa mutane za su sāke zauna a can,Za a kuma sāke gina biranen Yahuza.Waɗannan birane za su daina zama kufai.

Karanta cikakken babi Ish 44