Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 23:2-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Haka Ubangiji Allah na Isra'ila ya faɗa a kan makiyayan jama'arsa. “Kun warwatsar da garkena kun kore su, ba ku lura da su ba. Ni ma haka zan yi da ku saboda muguntarku, ni Ubangiji na faɗa.

3. Sa'an nan zan tattaro sauran garkena daga wuraren da aka warwatsa su, zan komo da su cikin garkensu, zan sa su hayayyafa su riɓaɓɓanya.

4. Zan sa makiyayan da za su lura da su. Ba kuwa za su ƙara jin tsoro, ko razana ba, ba kuma wanda zai ɓace, ni Ubangiji na faɗa.

5. “Ga shi, ni Ubangiji na ce, kwanakisuna zuwa,Sa'ad da zan tsiro da wani mai adalcidaga zuriyar DawudaWanda zai ci sarauta.Zai yi sarauta da hikima,Zai aikata abin da yake daidai aƙasar.

6. A zamaninsa za a ceci Yahuza,Isra'ila kuwa za ta zauna lafiya.Sunan da za a kira shi da shi kenan,‘Ubangiji Adalcinmu.’

7. “Saboda haka, ga shi, kwanaki suna zuwa, ni Ubangiji na faɗa, sa'ad da mutane ba za su ƙara cewa, ‘Na rantse da ran Ubangiji wanda ya fito da jama'ar Isra'ila daga cikin ƙasar Masar ba,’

8. amma za su ce, ‘Na rantse da ran Ubangiji wanda ya fito da zuriyar Isra'ila daga ƙasar arewa, daga kuma dukan ƙasashen da ya warwatsa su!’ Sa'an nan za su zauna a ƙasarsu ta kansu.”

9. A kan annabawa kuwa, zuciyata takarai,Dukan ƙasusuwana suna kaɗuwa,Saboda Ubangiji da kuma maganarsamai tsarki.Na zama kamar mashayi, wanda yabugu da ruwan inabi,

10. Gama ƙasar cike take da mazinata,Saboda la'ana, ƙasar za ta yimakoki,Wuraren kiwo na jeji sun bushe,Manufarsu mugunta ce,Ba su mori ƙarfinsu a inda yakamata ba.

11. “Annabi da firist, dukansu biyumarasa tsoron Allah ne,Har a cikin Haikalina na tarar damuguntarsu.”Ubangiji ya faɗa.

12. “Saboda haka hanyarsu za ta zamada santsi da duhu,Inda za a runtume su, su fāɗi.Gama zai kawo musu masifa ashekarar da za su shahukuncinsu.”Ubangiji ya faɗa.

13. “A cikin annabawan Samariya,Na ga abu marar kyan gani.Da sunan Ba'al suke yin annabci,Suna ɓad da jama'ata Isra'ila

14. Amma cikin annabawa naUrushalima,Na ga abin banƙyama.Suna yin zina, suna ƙarya,Suna ƙarfafa hannuwan masu aikatamugunta,Saboda haka ba wanda ya juya gabarin muguntarsa,Dukansu suna kama da Saduma,Mazaunanta kuwa kamarGwamrata.”

15. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce a kan annabawa,“Ga shi, zan ciyar da su da abincimai ɗaci,In shayar da su da ruwan dafi.Daga wurin annabawan UrushalimaRashin tsoron Allah ya fito yamamaye dukan ƙasar.”

16. Ubangiji Mai Runduna ya ce wamazaunan Urushalima,“Kada ku kasa kunne ga maganarannabawa,Gama sukan cika kunnuwanku daƙarairayi.Suna faɗar ganin damarsu,Ba faɗar Ubangiji ba.

17. Suna ta faɗa wa waɗanda suke rainamaganar Ubangiji cewa,‘Za ku zauna lafiya!’Ga kowane mai bin nufin tattaurarzuciyarsa,‘Ba masifar da za ta same ka.’ ”

18. Irmiya ya ce, “Gama wane ne a cikin annabawan nan ya taɓa neman shawarar Ubangiji don ya fahimci maganarsa, ko kuwa wane ne ya taɓa kasa kunne don ya ji maganarsa?

Karanta cikakken babi Irm 23