Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 20:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da Fashur, firist, ɗan Immer, shugaban Haikalin Ubangiji ya ji Irmiya yana annabci a kan waɗannan abubuwa,

2. sai ya sa aka yi wa Irmiya dūka, aka kuma sa shi cikin turu a ƙofar Biliyaminu, a Haikalin Ubangiji.

3. Kashegari sa'ad da Fashur ya fitar da Irmiya daga turu, sai Irmiya ya ce masa, “Ubangiji ba zai kira ka Fashur ba, amma ya ba ka suna Magormissabib, wato razana ta kowace fuska.

4. Haka Ubangiji ya ce, ‘Ga shi, zan maishe ka abin tsoro ga kai kanka, da dukan abokanka. Abokan gābansu za su kashe su da takobi a kan idonka. Zan ba da dukan Yahuza a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai kwashe waɗansu ya kai bautar talala a Babila, ya kuma kashe waɗansu da takobi.

5. Banda haka kuma zan ba da dukan dukiyar wannan birni, da dukan ribarsa, da dukan abubuwa masu tamani, da dukan dukiyar sarakunan Yahuza, ga abokan gābansu, waɗanda za su washe su, su kama su, su kai Babila.

6. Kai kuma, Fashur, da dukan waɗanda suke a gidanka, za ku tafi bauta a Babila, za ku shiga Babila, a can za ku mutu, a can za a binne ku, kai da abokanka waɗanda ka yi wa annabcin ƙarya.’ ”

7. “Ya Ubangiji ka ruɗe ni, na kuwaruɗu,Ka fi ni ƙarfi, ka kuwa rinjaye ni.Na zama abin dariya dukan yini,Kowa yana ta yi mini ba'a.

8. Duk lokacin da zan yi magana,Nakan ta da murya in yi magana daƙarfi cewa,‘Hargitsi da hallakarwa!’Gama saboda maganar Ubangiji nazama abin zargi,Da abin ba'a dukan yini.

9. Idan na ce, ‘Ba zan ambaci Ubangijiba,Ban zan ƙara yin magana da sunansaba,’Sai in ji damuwa a zuciyata,An kulle ta a ƙasusuwana,Na gaji da danne ta a cikina,Ba zan iya jurewa ba.

10. Na ji mutane da yawa suna sa minilaƙabi cewa,‘Razana ta kowace fuska,’Suna cewa, ‘Mu la'anta shi!Mu la'anta shi!’Har ma da abokaina shaƙiƙaiSuna jira su ga fāɗuwata.Suka ce, ‘Watakila a ruɗe shi,Sa'an nan ma iya rinjayarsaMu ɗauki fansa a kansa.’

11. Amma Ubangiji kana tare da niKamar jarumi mai bantsoro,Don haka masu tsananta mini za suyi tuntuɓe,Ba za su rinjaye ni ba.Za su sha kunya ƙwarai,Gama ba za su yi nasara ba.Ba za a manta da su ba.

12. Ya Ubangiji Mai Runduna, maigwada adali,Mai ganin zuciya duk da tunani,Ka sa in ga sakayyar da za ka yimusu,Gama a gare ka nake kawoƙarata.”

13. Ku raira waƙa ga Ubangiji!Ku yabi Ubangiji!Gama ya kuɓutar da ran mabukacidaga hannun mugaye.

Karanta cikakken babi Irm 20