Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 13:5-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sai na tafi, na ɓoye shi a Yufiretis kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.

6. Bayan an ɗan daɗe, sai Ubangiji ya ce mini, “Tashi, ka tafi Yufiretis, ka ɗauko abin ɗamara wanda na umarce ka ka ɓoye a can.”

7. Sai na tafi Yufiretis, na haƙa na ɗauko abin ɗamara daga wurin da na ɓoye shi. Amma abin ɗamara ya lalace, ba shi da sauran amfani.

8. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

9. “Haka zan lalatar da alfarmar Yahuza da yawan alfarmar Urushalima.

10. Wannan muguwar jama'a, wadda ta ƙi jin maganata, wadda ta taurare, ta bi son zuciyarta, ta kuma bi gumaka ta bauta musu, ta yi musu sujada, za ta zama kamar abin ɗamaran nan, wanda ba shi da sauran amfani.

11. Gama kamar yadda abin ɗamara yakan kame tam a gindin mutum, haka na sa dukan mutanen Isra'ila da dukan mutanen Yahuza su manne mini domin su zama jama'a, da suna, da yabo, da daraja a gare ni, amma sun ƙi ji.”

12. “Sai ka faɗa musu wannan magana cewa, ‘Ni Ubangiji Allah na Isra'ila na ce, a cika kowane tulu da ruwan inabi.’ Su kuwa za su ce maka, sun sani sarai za a cika kowane tulu da ruwan inabi.

13. Sa'an nan za ka faɗa musu, Ubangiji ya ce, ‘Ga shi, zan sa dukan mazaunan ƙasar su bugu da ruwan inabi, wato sarakunan da suka hau gadon sarautar Dawuda, da firistoci, da annabawa, da dukan mazaunan Urushalima.

14. Zan sa su kara da junansu, iyaye maza da 'ya'yansu maza, in ji Ubangiji. Tausayi, ko juyayi, ko jinƙai ba za su sa in fasa hallaka su duka ba.’ ”

15. Ku kasa kunne, ku ji,Kada ku yi girmankai, gamaUbangiji ya yi magana.

16. Ku girmama Ubangiji Allahnku,Kafin ya kawo duhu,Kafin kuma ƙafafunku su yi tuntuɓea kan dutse, da duhu duhu,Sa'ad da kuke neman haske, sai yamaishe shi duhu,Ya maishe shi duhu baƙi ƙirin.

17. Amma idan ba za ku ji ba,Raina zai yi kuka a ɓoye sabodagirmankanku,Idanuna za su yi kuka ƙwarai, za suzub da hawaye,Domin an kai garken Ubangiji zuwabauta.

Karanta cikakken babi Irm 13