Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 6:4-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Za a jera manyan duwatsu jeri uku, da jeri ɗaya na katako, a kuma biya kuɗin aikin daga baitulmalin sarki.

5. A kuma kawo kwanonin nan na zinariya da na azurfa cikin Haikalin Allah, waɗanda Nebukadnezzar ya kwaso daga cikin Haikali a Urushalima ya kawo Babila, a komar da su, a mayar da su a Haikali a Urushalima, a ajiye kowanne a wurinsa a Haikalin Allah.”

6. Sarki Dariyus ya ce, “Zuwa ga Tattenai, mai mulkin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu, wato ma'aikatan hukuma na lardin Yammacin Kogi, ku nisance su.

7. “Ku ƙyale aikin Haikalin nan na Allah kawai, ku ƙyale masu mulkin Yahudawa da dattawan Yahudawa, su sāke gina Haikalin Allah a wurin da yake a dā.

8. Ina umartarku ku biya wa dattawan Yahuza kuɗin sāke ginin Haikalin nan na Allah, a biya mutanen nan cikakken kuɗin aiki daga baitulmalin sarki, wanda yake a lardin Yammacin Kogi, ba tare da ɓata lokaci ba.

9. A ba su duk abin da suke bukata, wato kamar 'yan bijimai, da raguna, da 'yan tumaki domin yi wa Allah na Sama hadayun ƙonawa, da alkama, da gishiri, da ruwan inabi, da man naɗawa yadda firistoci a Urushalima suke bukata, sai a ba su kowace rana banda fashi,

10. domin su miƙa wa Allah na Sama sadaka mai daɗin ƙanshi, su kuma yi addu'a saboda sarki da 'ya'yansa.

11. Na kuma umarta, cewa duk wanda ya karya wannan doka, sai a fitar da itace daga cikin gidansa, a fiƙe kan itacen, a tsire mutumin, sa'an nan a mai da gidansa juji.

12. Allah wanda ya sa sunansa ya kasance a Urushalima, ya hamɓarar da kowane sarki, ko al'umma waɗanda za su sāke wannan doka don su lalatar da Haikalin Allah da yake a Urushalima. Ni Dariyus na kafa wannan doka. Lalle ne a kiyaye dokata sarai.”

13. Saboda maganar sarki Dariyus, sai Tattenai mai mulkin lardin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu suka aikata abin da sarki Dariyus ya umarta da aniya.

14. Dattawan Yahuza suka yi nasarar ginin ta wurin wa'azin annabi Haggai da Zakariya ɗan Iddo. Suka gama ginin bisa ga umarnin Allah na Isra'ila, da umarnin Sairus, da Dariyus, da Artashate sarakunan Farisa.

15. An gama ginin Haikali a ran ashirin da uku ga watan Adar, a shekara ta shida ta sarautar sarki Dariyus.

16. Sai mutanen Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da sauran waɗanda suka komo daga bauta, suka yi bikin keɓe Haikalin Allah da murna.

17. A bikin keɓe Haikalin Allah, suka miƙa bijimai ɗari, da raguna ɗari biyu,da 'yan raguna ɗari huɗu. Suka kuma miƙa hadayu don zunubi saboda dukan Isra'ila, bunsurai goma sha biyu, bisa ga yawan kabilan Isra'ila.

18. Sai suka karkasa firistoci da Lawiyawa ƙungiya domin yin aikin Ubangiji a Urushalima kamar yadda aka rubuta a Attaura ta Musa.

Karanta cikakken babi Ezra 6