Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 6:11-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Na kuma umarta, cewa duk wanda ya karya wannan doka, sai a fitar da itace daga cikin gidansa, a fiƙe kan itacen, a tsire mutumin, sa'an nan a mai da gidansa juji.

12. Allah wanda ya sa sunansa ya kasance a Urushalima, ya hamɓarar da kowane sarki, ko al'umma waɗanda za su sāke wannan doka don su lalatar da Haikalin Allah da yake a Urushalima. Ni Dariyus na kafa wannan doka. Lalle ne a kiyaye dokata sarai.”

13. Saboda maganar sarki Dariyus, sai Tattenai mai mulkin lardin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu suka aikata abin da sarki Dariyus ya umarta da aniya.

14. Dattawan Yahuza suka yi nasarar ginin ta wurin wa'azin annabi Haggai da Zakariya ɗan Iddo. Suka gama ginin bisa ga umarnin Allah na Isra'ila, da umarnin Sairus, da Dariyus, da Artashate sarakunan Farisa.

15. An gama ginin Haikali a ran ashirin da uku ga watan Adar, a shekara ta shida ta sarautar sarki Dariyus.

16. Sai mutanen Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da sauran waɗanda suka komo daga bauta, suka yi bikin keɓe Haikalin Allah da murna.

17. A bikin keɓe Haikalin Allah, suka miƙa bijimai ɗari, da raguna ɗari biyu,da 'yan raguna ɗari huɗu. Suka kuma miƙa hadayu don zunubi saboda dukan Isra'ila, bunsurai goma sha biyu, bisa ga yawan kabilan Isra'ila.

18. Sai suka karkasa firistoci da Lawiyawa ƙungiya domin yin aikin Ubangiji a Urushalima kamar yadda aka rubuta a Attaura ta Musa.

19. A rana ta goma sha huɗu ga watan fari, sai waɗanda suka komo daga bauta suka kiyaye Idin Ƙetarewa.

20. Gama firistoci da Lawiyawa sun tsarkake kansu, suka kuwa tsarkaka, sai suka yanka ragon Idin Ƙetarewa saboda dukan waɗanda suka komo daga bauta, da kuma saboda 'yan'uwansu firistoci, da su kansu.

21. Mutanen Isra'ila waɗanda suka komo daga zaman talala suka ci tare da kowane mutumin da ya haɗa kai da su, ya kuma keɓe kansa daga ƙazantar al'umman ƙasar, domin ya bi Ubangiji Allah na Isra'ila.

22. Suka kuma kiyaye idin abinci marar yisti kwana bakwai da murna, gama Ubangiji ya sa su yi murna, ya kuma juyo da zuciyar Sarkin Assuriya wajensu, saboda haka ya taimake su da aikin Haikalin Allah, Allah na Isra'ila.

Karanta cikakken babi Ezra 6