Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 43:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan haka kuma sai ya kai ni ƙofar da take fuskantar gabas.

2. Sai ga zatin Allah na Isra'ila yana tahowa daga gabas. Muryar Allah ta yi amo kamar rurin teku. Duniya kuwa ta haskaka da zatinsa.

3. Wahayin da na gani ya yi kama da wahayin da na gani lokacin da ya hallaka birnin, kamar kuma wanda na gani a bakin kogin Kebar. Sai na fāɗi rubda ciki.

4. Zatin Ubangiji ya shiga Haikalin ta ƙofar gabas.

5. Ruhu kuwa ya ɗaga ni, ya kai ni a farfajiya ta can ciki, sai ga zatin Ubangiji ya cika Haikali.

6. Sa'ad da mutumin yake tsaye kusa da ni, sai Ubangiji ya yi magana da ni daga cikin Haikalin.

7. Ya ce mini, “Ɗan mutum, wannan wuri shi ne kursiyin sarautata da kilisaina, inda zan zauna tsakiyar mutanen Isra'ila har abada. Mutanen Isra'ila da sarakunansu ba za su ƙara ɓata sunana mai tsarki ta wurin bauta wa gumaka da gina siffofin sarakunansu da suka mutu ba,

8. ko kuwa ta wurin sa dokin ƙofarsu kusa da dokin ƙofata, da kuma ta kafa madogaran ƙofarsu kusa da nawa, sai dai katangar da ta yi mana tsakani. Sun ɓata sunana mai tsarki da ayyukansu masu banƙyama, don haka na hallaka su saboda sun sa na husata.

9. Yanzu sai su zubar da gumakansu da siffofin sarakunansu nesa da ni, ni kuwa zan zauna a cikinsu har abada.

10. “Kai kuwa ɗan mutum, sai ka bayyana Haikalin ga mutanen Isra'ila domin su kunyata saboda muguntarsu, ka kuma sa su auna fasalin Haikalin.

Karanta cikakken babi Ez 43