Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 20:27-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. “Domin haka, ya ɗan mutum, ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce, ‘Ni Ubangiji Allah, na ce kakanninku sun saɓe ni da ba su amince da ni ba.

28. Gama sa'ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su, sa'ad da suka ga kowane tudu da kowane itace mai ganye, sai suka miƙa hadayunsu a wuraren nan suka tsokane ni da hadayunsu. A wuraren ne suka miƙa hadayunsu na turare mai ƙanshi da hadayu na sha.’

29. Sai na ce, ‘Wane ɗakin tsafi kuke tafiya?’ Domin haka aka kira sunan wurin Bama, wato tudu.

30. Domin haka ka ce wa mutanen Isra'ila, ‘Ni Ubangiji Allah na ce za ku ƙazantar da kanku kamar yadda kakanninku suka yi? Za ku bi abubuwan da suka yi na banƙyama?

31. Sa'ad da kuke miƙa hadaya, kuna miƙa 'ya'yanku hadaya ta ƙonawa, kuna ƙazantar da kanku ta wurin gumakanku har wa yau, to, za ku iya tambayata, ya ku mutanen Isra'ila? Ni Ubangiji Allah ba na tambayuwa gare ku.

32. Tunanin nan da kuke yi a zuciyarku, cewa kuna so ku zama kamar sauran al'umma da kabilan ƙasashe, ku bauta wa itace da dutse, ba zai taɓa faruwa ba.’

33. “Hakika, ni Ubangiji Allah na ce, zan sarauce ku ƙarfi da yaji, da fushi,

34. da ƙarfi da yaji da fushi kuma, zan fito da ku daga cikin mutane, in tattaro ku daga sauran ƙasashe inda aka warwatsa ku.

Karanta cikakken babi Ez 20