Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 13:16-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Wato annabawan Isra'ila waɗanda suka yi annabci a kan Urushalima, suka ga wahayin salama dominta, ga shi kuwa, ba salama, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

17. “Kai kuwa ɗan mutum, sai ka ɗaure wa matan mutanenka fuska, waɗanda suke annabci bisa ga son zuciyarsu. Ka yi annabci a kansu,

18. ka ce, ‘Ubangiji Allah ya ce, kaiton matan da suke ɗinka wa mutane kambuna, suna yi wa mutane rawunan dabo bisa ga zacinsu don su farauci rayukan mutane. Za ku farauci rayukan mutanena, sa'an nan ku bar rayukan waɗansu don ribar kanku?

19. Kun saɓi sunana a cikin mutanena don a tafa muku sha'ir, a ba ku ɗan abinci. Kuna kashe mutane waɗanda bai kamata su mutu ba, kuna barin waɗanda bai kamata su rayu ba ta wurin ƙaryace-karyacen da kuke yi wa mutanena waɗanda suke kasa kunne ga ƙaryace-ƙaryacen.’

20. “Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce, ina gāba da kambunanku da kuke farautar rayuka da su. Zan tsintsinke su daga damatsanku, in saki rayuka waɗanda kuka farauto kamar tsuntsaye.

21. Zan kuma kyakketa rawunanku na dabo, in ceci mutanena daga hannunku, ba za su ƙara zama ganima a hannunku ba, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.

22. “Kun karya zuciyar adali ta wurin ƙaryarku, ko da yake ni ban karya zuciyarsa ba. Kun ƙarfafa wa mugu gwiwa, don kada ya bar hanyarsa ta mugunta, ya tsira.

23. Domin haka ba za ku ƙara ganin wahayin ƙarya ba, ko ku yi dūba. Zan ceci mutanena daga hannunku. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.”

Karanta cikakken babi Ez 13