Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 9:10-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ba mu yi biyayya ga Ubangiji Allahnmu ta wurin kiyaye dokokinsa ba, waɗanda ya ba mu ta hannun bayinsa annabawa.

11. Dukan Isra'ilawa sun karya dokokinka, sun kauce, sun ƙi bin maganarka. La'ana da rantsuwa waɗanda suke a rubuce cikin dokokin Musa, bawan Allah, sun kama mu domin mun yi maka zunubi.

12. Ya tabbatar da maganarsa wadda ya yi a kanmu da shugabanninmu waɗanda suka yi mulkinmu. Ya aukar mana da babban bala'i, gama a duniya duka ba a taɓa yin irin abin da aka yi wa Urushalima ba.

13. Kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, haka wannan bala'i ya auko a kanmu, duk da haka ba mu nemi jinƙan Ubangiji Allahnmu ba, ba mu daina aikata muguntarmu ba, ba mu lizimci gaskiyarka ba.

14. Domin haka Ubangiji ya shirya bala'i, ya kuma aukar mana da shi, gama Ubangiji Allahnmu mai adalci ne cikin dukan abin da ya aikata, amma mu ba mu bi maganarsa ba.

15. “Ya Ubangiji Allahnmu, kai ne ka fito da jama'arka daga ƙasar Masar da iko mai girma, da haka ka bayyana ikonka kamar yadda yake a yau, amma mun yi zunubi, mun aikata mugunta.

16. Ya Ubangiji, saboda dukan ayyukanka na adalci, ka huce daga fushinka da hasalarka da ka yi da birninka Urushalima, tsattsarkan tudunka. Gama saboda zunubanmu da muguntar kakanninmu, Urushalima da jama'arka sun zama abin ba'a ga waɗanda suke kewaye da mu.

17. Yanzu ya Allahnmu, ka ji addu'ar bawanka da roƙe-roƙensa. Sabili da sunanka da idon rahama ka dubi tsattsarkan wurinka wanda ya zama kango.

18. Ya Allahna, ka karkato kunnenka ka ji, ka buɗe idanunka ka ga yadda mu da birnin da ake kira da sunanka muka lalace. Ba cewa muna da wani adalci na kanmu shi ya sa muka kawo roƙe-roƙenmu ba, amma saboda yawan jinƙanka.

19. Ya Ubangiji, ka ji mu. Ya Ubangiji, ka garfarce mu. Ya Ubangiji, ka saurare mu, ka yi wani abu saboda sunanka. Ya Allahna, kada ka yi jinkiri domin da sunanka ake kiran birninka da jama'arka.”

20. Sa'ad da nake ta addu'a, ina faɗar zunubina, da na jama'ata Isra'ila, ina kawo roƙe-roƙena wurin Ubangiji Allahna saboda tsattsarkan tudun Allahna.

21. Sa'ad da nake yin addu'a, sai mutumin nan Jibra'ilu, wanda na gani a wahayin da ya wuce, ya zo wurina a gaggauce wajen lokacin yin hadaya ta maraice.

Karanta cikakken babi Dan 9