Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 4:11-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Itacen ya yi girma, ya ƙasaita,Ƙwanƙolinsa ya kai har sama,Ana iya ganinsa ko'ina a duniya.

12. Yana da ganyaye masu kyauDa 'ya'ya jingim don kowa da kowa ya ci.Namomin jeji suka sami inuwa a ƙarƙashinsa,Tsuntsayen sama kuma suka zauna a rassansa.Dukan masu rai a gare shi suka sami abinci.

13. “ ‘A cikin wahayin da na gani sa'ad da nake kwance a gado, sai ga wani mai tsaro, tsattsarka, ya sauko daga sama.

14. Sai ya yi magana da ƙarfi, ya ce,“A sare itacen, a daddatse rassansa,A zage ganyayensa ƙaƙaf, a warwatsar da 'ya'yansa.A sa namomin jeji su gudu daga ƙarƙashinsa,Tsuntsaye kuma su tashi daga rassansa.

15. Amma a bar kututturen da saiwoyinsa a ƙasaƊaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla.A bar shi can cikin ɗanyar ciyawar saura,Ya jiƙe da raɓa,Ya yi ta cin ciyawa tare da namomin jeji.

16. A raba shi da hankali irin na mutane,A ba shi irin na dabba.Zai zauna a wannan hali har shekara bakwai.

17. Wannan shi ne hukuncin da tsarkaka,Masu tsaro suka shawarta,Suka yanke domin masu rai su saniMaɗaukaki yake sarautar 'yan adam,Yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama,Yakan sa talaka ya zama sarki.”

18. “ ‘Mafarkin da ni sarki Nebukadnezzar na yi ke nan. Kai Belteshazzar kuma, sai ka faɗa mini ma'anarsa, domin dukan masu hikima na cikin mulkina ba su iya faɗar mini ma'anar, amma kai ka iya, gama ruhun alloli tsarkaka yana cikinka.’ ”

19. Daniyel kuwa wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, ya tsaya zugum da ɗan daɗewa, tunaninsa ya ba shi tsoro. Sarki ya ce, “Belteshazzar, kada ka bar mafarkin ko ma'anarsa ya ba ka tsoro.”Sai Belteshazzar ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, Allah ya sa mafarkin nan, da ma'anarsa, su zama a kan maƙiyanka.

20. Itacen nan da ka gani wanda ya yi girma, ya ƙasaita, ƙwanƙolinsa ya kai sama, har ana iya ganinsa daga ko'ina a duniya,

21. yana da ganyaye masu kyau da 'ya'ya jingim don kowa da kowa ya ci, namomin jeji suka sami inuwa a ƙarƙashinsa, tsuntsaye kuma suka zauna a rassansa,

22. kai ne wannan itace, ya sarki. Ka yi girma, ka ƙasaita. Girmanka ya kai har sama, mulkinka kuma ya kai ko'ina a duniya.

23. Ka kuma ga mai tsaro tsattsarka yana saukowa daga sama, yana cewa a sare itacen nan, a ragargaje shi, amma a bar kututturen da saiwoyinsa cikin ƙasa ɗaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla. An ce a bar shi can a ɗanyar ciyawar saura, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namomin jeji har shekara bakwai.

24. “Ga ma'anarsa, ya sarki, wannan ƙaddara ce wadda Maɗaukaki zai aukar wa shugabana sarki da ita.

Karanta cikakken babi Dan 4