Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 7:8-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ya tambaye ni, ya ce, “Amos, me ka gani?”Sai na ce, “Igiyar awon gini na gani.”Ya kuma ce,“Duba, da wannan zan nuna yaddajama'ata sun zama kamar bangonda ya karkace.Ba zan sāke nufina a kan yi musuhukunci ba.

9. Zan hallakar da wuraren sujada nazuriyar Ishaku.Za a hallakar da tsarkakan wurare naIsra'ila.Zan fāɗa wa zuriyar sarkiYerobowam da yaƙi.”

10. Amaziya, firist, na Betel kuwa, ya tafi ya faɗa wa Yerobowam Sarkin Isra'ila, ya ce, “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a cikin jama'ar Isra'ila. Maganganunsa za su hallakar da ƙasar.

11. Abin da ya faɗa ke nan, ‘Za a kashe Yerobowam a bakin dāga, a sa jama'ar Isra'ila su yi ƙaura zuwa wata ƙasa.’ ”

12. Amaziya kuwa ya ce wa Amos, “Kai maƙaryaci ne na ainihi! Koma ƙasar Yahuza ka nemi abin zaman gari, ka yi ta annabcinka a can.

13. Amma a nan Betel kada ka ƙara yin annabci. Nan wurin yin sujada na sarki ne, haikali ne na al'umma.”

14. Sai Amos ya amsa ya ce, “Ni ba annabi ba ne. Wannan ba aikina ba ne. Ni makiyayi ne, mai kuma lura da itatuwan ɓaure.

15. Amma Ubangiji ya raba ni da aikina na kiwo, ya umarce ni in tafi in yi magana da jama'arsa, wato Isra'ila.

16. Domin haka, sai ka kasa kunne ga abin da Ubangiji ya ce. Saboda ka ce mini in daina yin annabci gāba da jama'ar Isra'ila, kada kuwa in yi wa zuriyar Ishaku ɓaɓatu,

Karanta cikakken babi Amos 7