Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 7:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A wahayin da Ubangiji ya nuna mini, sai na ga ya yi cincirindon fara nan da nan bayan da aka ƙarasa yankan rabon ingiricin da yake na sarki, ciyawar kuma ta soma tohuwa.

2. A wahayin, na ga fara ta cinye kowane ɗanyen ganye a ƙasar. Sai na ce,“Ka gafarta wa jama'arka, yaUbangiji!Ƙaƙa za su tsira?Ga su 'yan kima ne, marasaƙarfi.”

3. Ubangiji kuwa ya dakatar danufinsa,Ya ce, “Abin da ka gani, ba zai faruba.”

4. A wahayin da Ubangiji ya nuna mini, na gan shi yana shirin hukunta jama'arsa da wuta. Wutar ta ƙone babbar teku, har ma ta fara ƙone ƙasar.

5. Sa'an nan na ce,“Ya Ubangiji, in nufinka ne ka bari!Ƙaƙa jama'arka za su tsira?Ga su 'yan kima ne, marasaƙarfi.”

6. Ubangiji kuwa ya dakatar da nufinsa, ya ce,“Wannan ma ba zai faru ba.”

7. Ubangiji kuma ya nuna mini wani wahayi. A wahayin sai na gan shi, yana tsaye kusa da bangon da ake ginawa. Yana riƙe da igiyar awon gini.

8. Ya tambaye ni, ya ce, “Amos, me ka gani?”Sai na ce, “Igiyar awon gini na gani.”Ya kuma ce,“Duba, da wannan zan nuna yaddajama'ata sun zama kamar bangonda ya karkace.Ba zan sāke nufina a kan yi musuhukunci ba.

9. Zan hallakar da wuraren sujada nazuriyar Ishaku.Za a hallakar da tsarkakan wurare naIsra'ila.Zan fāɗa wa zuriyar sarkiYerobowam da yaƙi.”

10. Amaziya, firist, na Betel kuwa, ya tafi ya faɗa wa Yerobowam Sarkin Isra'ila, ya ce, “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a cikin jama'ar Isra'ila. Maganganunsa za su hallakar da ƙasar.

11. Abin da ya faɗa ke nan, ‘Za a kashe Yerobowam a bakin dāga, a sa jama'ar Isra'ila su yi ƙaura zuwa wata ƙasa.’ ”

12. Amaziya kuwa ya ce wa Amos, “Kai maƙaryaci ne na ainihi! Koma ƙasar Yahuza ka nemi abin zaman gari, ka yi ta annabcinka a can.

13. Amma a nan Betel kada ka ƙara yin annabci. Nan wurin yin sujada na sarki ne, haikali ne na al'umma.”

Karanta cikakken babi Amos 7