Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 7:2-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Firistoci ba su iya shiga Haikalin Ubangiji ba saboda darajar Ubangiji ta cika Haikalin.

3. Sa'ad da dukan Isra'ilawa suka ga wuta ta sauko daga sama, ɗaukakar Ubangiji kuma na cike da Haikalin, sai suka sunkuyar da kansu ƙasa, suka yi sujada, suka yabi Ubangiji, saboda nagarinsa da madawwamiyar ƙaunarsa.

4. Sa'an nan sarki da dukan jama'a suka miƙa hadaya a gaban Ubangiji.

5. Sarki Sulemanu kuwa ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin da dubu biyu (22,000), da tumaki dubu ɗari da dubu ashirin (120,000). Ta haka sarki tare da dukan jama'a suka keɓe Haikalin Allah.

6. Sai firistoci suka tsaya a matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a nasu matsayi riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji, gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce har abada. A duk lokacin da Dawuda zai yabi Ubangiji tare da su, sai firistoci waɗanda suke daura da su su busa ƙaho, sa'an nan sai dukan Isra'ilawa su miƙe tsaye.

7. Sa'an nan Sulemanu ya tsarkake tsakiyar filin da yake a gaban Haikalin Ubangiji, gama a wurin ne ya miƙa hadayun ƙonawa da kitsen hadayu domin salama, saboda bagaden tagulla wanda Sulemanu ya yi bai iya ɗaukar hadayu domin ƙonawa, da ta gari, da ta kitse ba.

8. A wannan lokaci, Sulemanu ya yi biki a wurin har kwana bakwai, tare da dukan Isra'ilawa, da waɗanda suka zo tun daga ƙofar Hamat, har zuwa rafin Masar, taron kuwa mai girma ne ƙwarai.

9. A rana ta takwas kuwa suka yi wani muhimmin taro, domin su keɓe bagaden. Sun yi kwana bakwai suna yin bikin.

Karanta cikakken babi 2 Tar 7