Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 6:23-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. sai ka ji ka yi wa bayinka shari'a daga Sama, ka hukunta wa mugun, ka ɗora masa alhakinsa, ka baratar da adalin, ka ba shi sakayyar adalcinsa.

24. “Idan abokan gāba sun kori jama'arka, wato Isra'ila, saboda laifin da suka yi maka, sa'an nan suka juyo suka shaida sunanka, suka yi addu'a, suka yi roƙo a gabanka a wannan Haikali,

25. sai ka ji daga Sama ka gafarta zunubin jama'arka Isra'ila, ka komo da su ƙasar da ka ba su, su da kakanninsu.

26. “Sa'ad da aka kulle sammai, ba ruwan sama saboda sun yi maka zunubi, sa'an nan suka fuskanci wurin nan suka yi addu'a, suka shaida sunanka, suka juyo suka daina zunubinsu a sa'ad da ka hukunta su,

27. sai ka ji daga Sama ka gafarta zunubin bayinka, wato jama'arka Isra'ila, lokacin da ka koya musu kyakkyawar hanya da za su bi. Sai ka sa a yi ruwa a ƙasarka, wadda ka ba jama'arka gādo.

28. “Idan ana yunwa a ƙasar, ko annoba, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fārā, ko gamzari, ko da maƙiyansu za su kewaye biranensu da yaƙi, ko kowace irin annoba, da kowace irin cuta da take akwai,

29. kowace irin addu'a, kowane irin roƙo da kowane mutum, ko jama'ar Isra'ila suka yi, ko wannensu yana sane da irin wahalarsa, da baƙin cikinsa, ya kuwa ɗaga hannunsa wajen wannan Haikali,

30. sa'an nan za ka ji daga wurin zamanka a Sama, ka yi gafara, ka kuwa sāka wa kowa bisa ga al'amuransa, wanda ka san zuciyarsa, gama kai kaɗai ne ka san zukatan mutane,

31. don su yi tsoronka su yi tafiya bisa ga dokokinka muddin ransu, a ƙasar da ka ba kakanninmu.

32. “Haka kuma baƙo wanda ba cikin jama'arka Isra'ila yake ba, idan ya taho daga wata ƙasa mai nisa saboda girman sunanka da ƙarfin ikonka, in ya zo ya yi sujada, yana fuskantar Haikalin nan,

33. ka ji daga Sama wurin zamanka, ka kuwa aikata bisa ga dukan irin roƙon da baƙon ya yi gare ka. Domin ta haka sauran al'umman duniya za su san sunanka, su kuma yi tsoronka, yadda jama'arka Isra'ila suke yi, za su kuma sani cewa wannan Haikali da na gina, ana kiransa da sunanka.

34. “Sa'ad da jama'arka za su fita don yin yaƙi da magabtansu, duk dai ko ta ina ne za ka aike su, in sun yi addu'a gare ka, suna fuskantar wannan birni wanda kai ka zaɓa, da Haikalin nan da na gina saboda sunanka,

35. sai ka ji addu'arsu da roƙe-roƙensu daga Sama, ka biya muradinsu.

36. “Sa'ad da suka yi maka zunubi (gama ba wani ɗan adam da ba ya yin zunubi), ka kuwa yi fushi da su, har ka bashe su a hannun magabtansu, magabtansu suka kakkama su suka kai wata ƙasa ta nesa ko ta kusa,

Karanta cikakken babi 2 Tar 6